03/11/2022
BANKUNAN GWAMNATI DA MANUFAR BUDE SU.
Akwai Bankuna na gwamnati wadda aka kafa su don tallafi da bunkasa tattalin arzikin kasa na ýan najeriya k**ar haka;
1. Nigerian Bank of Industry. Wato banki domin kampuna masu kere kere.
2. Development Bank of Nigeria. Wato banki domin tallafi ga duk wani da Allah yayi wa baiwa dan najeriya wadda in an tallafa masa zai ampanar da kansa kuma ya ampanar da tattalin arzikin kasan najeriya.
3. Morgage Bank of Nigeria. Wato banki domin sauwakawa ma ýan najeriya su mallaki muhallin kansu.
4. Nigerian Bank of Agriculture. Wato banki domin tallafawa manoma da abunda ke da alaka da noma k**ar kiwo.
5. Central Bank of Nigeria. Wato bankin baitul mal. Bankin da take kulawa da dukiyar kasa. Bankin bankuna. Banki me bada lasin, reno, kulawa, tarbiyyarwa da ladabta sauran bankuna na jari hujja. Banki mai kololon iko akan kudin najeriya.
Dukanin bankunan da muka ambata a sama na gwamnati ne. Amma duk sare saren tallafin su angina su ne akan 'riba' wato kudin ruwa. Kuma duk musulmi komin raunin imanin sa ya k**a ta ya kyamachi kudin ruwa. Sabi da Allah baiyi sausauchi akai ba. A dalilin haka sai musulmai ýan arewa s**a samu sanyin guiwwa wajen moran wannan bankuna. Kuma ba asamu chikekken bayani da ga wajen malammu da suke da ido me zurfi a addini da kuma ilimin tattalin arziki ba.
MAFITA;
Dole malaman mu irinsu Sanusi Lamido Sanusu, Dr Bashir Aliyu, Prof. Isa Ali Pantami, As. Prof. Mansur Isa yelwa, Dr. Jabir Maihula, malaman malamammu irin su Dr Sani Umar Rijiyan Lemu, Sheikh Abdurrazzak Yahaya Haifan, Sheikh Adamu Dokoro, Dr. Idris Bauchi, Malam Musa Adam Maihula, matasan malamai irinsu Sheikh Musa Yusuf Asadussunna, Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe Barden Sunnah, Lawan Triump Kano da sauran malamai da na sani da wadda ban sani ba su sa gwamnati agaba sai an sara bankunan nan da na ambata a sama suyi mana sari na mu'amala da su babu kudin ruwa. Domin hakan hakkinmu ne.
GODIYA;
Duk da chewa kwalliya bata biya kudin sabulu ba, muna godiya ga Khalifa Sanusi Lamido Sanusi, Dr Bashir Aliyu da sauran malaman da suke kokarin promoting Islamic Banking and Finance a Najeriya.
Allah ya saka da alheri.
Sani Bashiru Ali
08036920230