05/02/2026
GUINNESS: MATASHI YA KAFI TARIHI NA FUSKA MAFI CIKIN GASHI A DUNIYA
Hukumar Guinness World Records ta bayyana wani matashi mai suna Lalit Patidar a matsayin wanda ya kafa tarihi na mutum mafi fuska cike da gashi a duniya.
Rahotanni sun nuna cewa sama da kashi 95 cikin 100 na fuskarsa na cike da gashi, sakamakon wani yanayi na halitta da yake da shi tun haihuwa. Wannan lamari ya sanya shi cikin manyan mutanen da s**a kafa tarihin duniya.
Lalit Patidar ya bayyana cewa yana jin daɗin yadda Allah ya halicce shi, inda ya ce: “Ina son yadda nake, kuma bana son canza kamannina.”
Duk da kalubalen da ke tattare da bambancin kamanni, Lalit ya zama abin koyi wajen karɓar kai da yarda da halitta, lamarin da ya janyo hankalin jama’a a sassan duniya.