23/07/2024
WANENE ƊAN AGAJI ?
ƊAN AGAJI SHINE:- Wanda Ya sadaukar da kansa don yi wa addinin Allah Hidima da taimakawa da kyautatuwar mu'amalar al'ummar musulmi, ba tare da neman Sakamakon duniya ba, to wannan shine ɗan Agaji na haƙiƙa a Musulunci. Shine wanda ya shiga cikin masu bin umurnin Allah (SWA) a cikin Alƙur'aninsa mai girma, Cewa;
وتعاونوا على البرّ والتقوى ولا تعاونوا على الإثم والعنوان واتقوا الله إنّ الله شديد العقابِ.
"Kuma ku taimaki juna a kan aikin ƙwarai sa taƙawa. Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da Zalunci, Kuma kubi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah ne Allah mai tsananin uƙuba ne"(SURATUL MA'IDAH:2)
Har ila yau kuma mai irin wannan aiki na agaji ya kasance daga cikin zaɓaɓɓun bayi da Allah (SWA) Yayi musu shaida da cewa;
ولتكن منكم أمَّةٌ يدعون إلى الخير ويأمرون بالمعروف وينهون عن المنكر وأُولدك هم المفلحون.
"Kuma wata jama'a daga cikin ku su kasance suna ƙira zuwa ga alheri, kuma suna umarni da kyawawan ayyuka, kuma suna hani daga abinda ake ƙi. Kuma waɗannan, sune masu cin nasara "(SURATUL ALI IMRAN :104
A bisa bayanan da ya gabata dangane da nau' oin ayyukan Agaji, zamu iya fito da ma'anar ɗan Agaji don mu fahimci ko wanene ɗan Agaji a musulunci.
Ɗan Agaji, anan yana nufin duk wani musulmi da ya rungumi aikin sa kai wadda ya ciki sharuɗɗa Kamar haka:
1. Ya kasance an tsarkake niyya wajen aikin da ɗan Agaji zai yi, Ya wajaba ya zama don neman yardan Allah , amma ba saboda neman wata riba ta duniya ba.
2. Ya kasance aikin na ɗa'a ga Allah ne, wadda ya dace da abin da Allah yake so kuma bisa koyarwar Annabi (SAW). Ƙirƙirarrun ayyuka da kuma ayyukan da s**a fita daga ɗa'ar Allah ba za a ƙira su ayyukan Agaji a Musulunci ba.
Allah muke roƙo Ya datar damu muyi gamo da katar da alkhairi yasanya mana ikhlasi cikin ayyukanmu mu.
Ɗan uwanku masoyin ku
Shu'aibu MMai(Abu Ja'afar)
17/01/1446H
23/07/2024M