Waziri Masjeed Lawan Musa Ward Bade, Yobe State.

Waziri Masjeed Lawan Musa Ward Bade, Yobe State. Ramadan Tafsirin 1443

17/11/2025
25/09/2024

Assalamualaikum warahmatullahi wabarkahu.
Dukkan yabo ya tabba ga Allah. Muna godiya a gare shi, muna neman taimakonsa, muna neman gafararsa, Kuma muna neman tsiransa daga sharrace - sharracen rayukanmu da miyagun ayyukanmu. Wanda Allah ya shirye shi babu mai batar dashi, wanda kuma Allah ya batar babu mai shiryar dashi. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai, babu abokin tarayya a gare shi, kuma ina shaidawa cewa annabi Muhammadu (S.A.W) Bawansa ne kuma Manzonsa ne. Allah yayi tsira a gare shi da alayensa da sahabbansa da wadanda s**a bisu da kyakkyawan kwaikwayo har izuwa ranar kiyama, kuma ya yi musu aminci mai yawa.
Bayan haka, Ina mika sakon gaisuwa tare da fatan alkhairi ga Malam Isa Ibrahim Gashua Hafidhahullah. (Zonal Commander of Hisbah Yobe State). Duba da irin namijin kokari da yakeyi wajen sadaukar da lokacin sa wajen karantarwa ba dare ba rana da kuma umarni da kyakkyawan aiki da kuma hani ga mummuna.
Ni Usman Muhammad Bala a madadin dalibanka da ke masallacin waziri bayan Umar Suleiman Central Primary School Gashua.

Ina mika sakon godiya a madadin dalibanka dake masallacin waziri da ma al'umar unguwa baki daya. Kamar yadda muka Sani cewa duk sati Malam Yana karantar damu a wannan masallaci mai tarin albarka a ranaku kamar haka: Asabar ayi "MUWADDA MALIK" Lahadi kuma ayi "RIYADUSSALINA" NA IMAMUN NAWAWI. Sannan idan Ramadan yazo ya kan gudanar da tafsirin Al-Qur'ani mai girma, a rana Ranar Lahadi data gabata ne 19/03/1446A.H Wanda yayi dai-dai da 22/09/2024. Karkashin jagorancin Malam Isa Ibrahim Gashua Hafidhahullah Allah ya bamu ikon Kamala karatun RIYADUSSALINA NA IMAMUN NAWAWI a darasi na dari biyu da goma sha Tara (219) a wannan masallaci na WAZIRI. Wannan littafin anfarashine bayan kammala kitabul akhdari.
Anfara "RIYADUSSALINA" 4/04/1441A.H / 1/12/2019G. Wanda yayi dai-dai da shekara hudu da wata goma sha daya da kwanaki goma sha shida (4years - 11months and 16 days). Muna rokon Allah yasa mu amfana da abinda muka koya.

12/03/2024

Assalamualaikum warahmatullahi ta'ala Wa barakatuhu.
Kamar yadda aka saba haska tafsirin Al-qur'ani Mai girma Wanda Malam Isah Ibrahim yake gabatarwa yauma in Sha Allah. Za'a fara gudanarwa. Allah ya bada ikon saurare Ameen

07/01/2024

MACEN KWARAI TANA DAKIN MIJINTA

Inajin tsoro kuma ina mamaki yadda Al'ummar mu ta gafala da mayar da hankali akan kallon films ,maza da mata yara da manya adai dai lokacin da qiyama take matsowa,rayuwa tana tsada ,abin da za'aci da kyar ,amma a lokacin muke mayar da hankalinmu akan fina finai masu shagaltarwa ,Series bayan series ,babu ranar da zai kare ballantana kuma adena . A yau mutum yana iya bibiyar series film se
series bayan series amma bazai iya bibiyar tafser din sati ko karatun wani littafi daban ,Yau da manzan Allah zaiga wannan Al'umma da zaiyi mamaki ace wannan al'umma ce da ya shafe shekaru 23 yana karantar da ita ,babu mamaki maganar Allah ne yake bayyana dama Allah ya fadi irin haka zata bayyana dab da tashin qiyama A cikin suratul anbiya, Allah yasa mudace Ameeen

Address

Lawan Musa
Gashua
88448

Telephone

+2347066868667

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Waziri Masjeed Lawan Musa Ward Bade, Yobe State. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Waziri Masjeed Lawan Musa Ward Bade, Yobe State.:

Share