Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah Jibwis Bagari Funtua

  • Home
  • Nigeria
  • Funtua
  • Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah Jibwis Bagari Funtua

Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah Jibwis Bagari Funtua لا طاعة لمن لم يطع الله عز وجل

27/01/2026
26/01/2026

WA'AZIN SATI UKU-UKU

JUMU'A daga ita sai azumi za'ai wa'azi a MASJID ABU UBAIDAH AMIR BINIL-JARRAH
Mal.Salisu Khalil zaiyi karatu

26/01/2026

ALHAMDULILLAH

Masha Allah media II
10/12/2025

Masha Allah media II

Masha Allah. Wannan sune sabbin zababbun media team na Izalah Bagari Funtua.Ku tayamu da addu'ar yada alkhairi na sunnah...
10/12/2025

Masha Allah. Wannan sune sabbin zababbun media team na Izalah Bagari Funtua.
Ku tayamu da addu'ar yada alkhairi na sunnah iya tsawon lokaci mu.

Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta tarayyar Najeriya Sheikh (Dr.) Abdullahi Bala Lau ya tu...
10/12/2025

Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta tarayyar Najeriya Sheikh (Dr.) Abdullahi Bala Lau ya turo tawaga ta musamman Jihar Katsina

Daga: Yusuf Hassan Buhari

Da safiyar yau Talata 17 Jumada Thani, 1447 wanda yayi daidai da 09 Disamba, 2025 Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Katsina Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus-Sunnah) ya karbi bakuncin tawagar Shugaban Kungiyar na Kasa, Sheikh (Dr.) Abdullahi Bala Lau

Jagoran tawagar Daraktan Agaji na Kasa, Engr. Mustapha Imam Sitti ya bayyana cewa Shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau ya turo wannan tawaga ne ta zo Katsina domin dubiyar rashin lafiya da wasu daga cikin manyan maluman wannan Kungiya mai albarka da ke wannan Jiha ta Katsina bisa jarabawar rashin lafiya da su ke fama da ita wato Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa Sheikh Barr. Ibrahim Sabi'u Jibia wanda ya samu jarabawar karaya a kafarsa da kuma Shugaban Kwamitin Ayyuka na Kasa Sheikh Habibu Yahayya Kaura wanda ke fama da rashin lafiya ya ke kwance yanzu haka a asibitin koyarwa da ke Garin Katsina

A nashi jawabin Shugaban Kungiyar na Jihar Katsina Sheikh Sautus-Sunnah bayan godiya ga Allah (S.W.A) ya bayyana jin dadin shi da yin godiya bisa wannan tawaga da Shugaba ya turo ku domin jajanta mana bisa rashin lafiya da wadannan bayin Allah su ke cikin ta

Muna rokon Allah ya saka maku da alkhairi ya baku ladar sada wannan zumunci da akai su kuma muna rokon ya ba su lafiya ya kuma sanya kaffara ne

Bayan nan tawagar ta wuce gidan Sheikh Barr. Ibrahim Sabi'u Jibia domin duba lafiyarshi tare da isar da sakon Shugaba. Daga nan tawagar ta wuce asibitin koyarwa inda ta duba Sheikh Habibu Kaura shi ma domin duba yana yin na shi jikin inda yake karbar magani da dubawa ta musamman a asibitin koyarwa da ke cikin Garin Katsina

Tawagar wadda Daraktan Agaji na Kasa din ke jagoranta inda Shugaban Kungiyar na Jihar Kaduna Alh. Adamu Ibrahim da Shugaban Majalisar Malamai na Jihar Kaduna Imam Aliyu Abdullahi Talex su ka rufa ma shi baya

Inda su ka samu tarba daga Sakataren Majalisar Agaji ta Kasa Alh. Abba Yahayya, Daraktan Agaji na Jihar Katsina Alh. Garba Galadima Charanchi, P.R.O na Majalisar Agaji ta Kasa Alh. Aliyu Sani Abubakar, Auditor na Majalisar Agaji ta Kasa Alh. Sulaim Abukur, Shugaban Kwamitin matasa na Jiha Sheikh Safiyyu Alkasim Saulawa, Dr. Abdurrahim Sabi'u Rafin Dadi

Jibwis Nigeria

09/12/2025

Mal. Abusufyan Sani Zuma kenan ke tunatar damu gameda sallar gawa.

Allah saka da alkhairi yajikan mamatanmu ameen.

Jibwis Bagari

Address

Umar Bin Khattab Mosque, Beside Taritil Qur'an School, Bagari Central, Bagari Funtua
Funtua

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah Jibwis Bagari Funtua posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share