29/07/2025
HAƊIN KAN MUSULMI
Babu shakka akwai alfanu da yawa a wannan aiki da Maulanmu Prof. Ibrahim Maqari ya ɗauka kuma a baya-bayan nan ziyarar da ya kai Jihar Gombe babbar alama ce da take nuna hakan.
Masu sukar hakan a da'irar ɗariqa sun kasu biyu a nawa hangen:
1- Masu yi da kyakkyawar niyya da kuma ƙauna da suke wa Jagoran da kuma mabiya kada hakan ya buɗe ƙofar da zata sanya ayi sako-sako da muhimman sharuɗɗa na ɗariqar, wanda hakan na iya zama dalili na fita daga ɗariqar.
2- Masu yi da wata manufa wadda manufofin iri-iri ne, basai na tsawaita akai ba.
To aikin da yake kan Maulana Prof. Shine cigaba da wayar da kai cikin hikima da kuma buɗe ƙofar tattaunawa ga waɗanda suke kaso na farko domin jin irin hujjojinsu da kuma naqasha wannan hujjojin ta yanda za a samu fahimtar juna domin ƴan uwanka ne na Allah kuma masoya.
Abbas Sadauki
4-Safar-1447
28-7-2025