01/07/2026
WA'AZIN WALIMAR AURE GA 'YAN UWA MUSULMI MATA
A madadin 'yan uwa da aminai na Ango da Amarya,
muna farin cikin gayyatar Al'ummar Musulmi Mata kaɗai zuwa babban taron:
WA'AZIN WALIMA
Wanda za a gudanar domin Munasabar Auren
GONI IMAM DR. NASIR ABDURRAHMAN FUNTUA
Da Za'a daura ranar Juma'a 03-07-2026 .
A Masallacin Juma'a JIBWIS Zaria Road Funtua
Za a samu halartar manyan malamai da Gonaye Alƙur'ani mai girma domin gabatar da muhimman nasihohi da wa'azuzzuka masu amfani.
A ƙarƙashin jagorancin:
Sheik Abdulbasir Unguwar Mai Kawo
Rana: Alhamis 02-07-2027
Lokaci: 4:30 na yamma
Wuri: Dakin Taro na Sheikh AbdurRahm Ahmad, Unguwar Wanzamai Funtua
Muna gayyatar dukkan 'yan uwa Musulmi mata da su kasance wannan Wa'azin domin samun albarka da fa'ida daga wannan zama mai albarka.
Allah Ya sanya wannan walima ta zama sanadin alheri, zaman lafiya da albarka ga ma'aurata.
SHIRYAWA: MANYAN AMINAN ANGO.
• Goni Abubakar Sa'eed Musa Funtua
• Sheik Usman Rasheed Funtua Almadany
Azo da wuri domin amfana da wannan babban taro.
Za mu kawo muku taron kai-tsaye a
Funtua Islamic Channel
Da sauran shafukan da muke kwance da su.