Funtua Islamic Channel

Funtua Islamic Channel Mun bude wannan shafi ne domin fadakarwa, Ilmantarwa da nishadantarwa abisa koyarwar addinin Musulunc

MAJLIS AL-USUL WA AL-QAWA'ID LI-SHEIKH THALITH KHALIL BIN ALI AL-MADNI. Na gayyatar Al-Ummar Musulmi Maza da Mata zuwa b...
28/08/2026

MAJLIS AL-USUL WA AL-QAWA'ID
LI-SHEIKH THALITH KHALIL BIN ALI AL-MADNI.

Na gayyatar Al-Ummar Musulmi Maza da Mata
zuwa babban taron
WA'AZIN MUSULUNCI NA DUNIYA
Domin karfafa zumunci, hadin kai da 'yan uwantakar Musulmi.

Wanda in sha Allah Za'ayi kamar haka:

NA MATA
RANA: Asabar, 29 ga Agusta, 2026
LOKACI: 4:30pm Na yamma
WURI: Masallacin Juma'a na Makera, Funtua,

NA MAZA
RANA: Asabar, 29 ga Agusta, 2026
WURI: Masallacin Juma'a na Makera, Funtua,
LOKACI: Bayan Sallar Magarib

MALAMAI MASU WA'AZI:

1. Prof. Mansur Isah Yelwa, ESQ
2. Dr. Umar Garba Dokaj
3. Mal. Umar Shehu Aliyu
4. Malam Abubakar Musa Giade

MASU GAYYATA:
1. Shekh Salisu Khalii Aliyu Almadany.
2. Sheikh Ishaq Umar Abduliahi Almadny
3. Dr. Ismail Salisu Abdullahi Almisry

SHUGABAN ZAMA
Shelkh muhd Aliyu Bako shugaban malisar malamal JIBWIS Funtua LGA Katsina state

Allah ya bada ikon halarta Amin.

✍️
Nasiru Sulaiman Funtua
JIBWIS Social media Funtua

28/08/2026

Cigaba da tafsirul alkur ani maigirma daga masjid allulbaiti wasahbah

28/08/2026

KAI TSAYE

KHUDUBAR JUMA'A DAGA

MASALLACIN DAN LIMAN
DUTSEN REME BYE PASS UNGUWAR DAHIRU

DAGA
IMAM NURA MUSA UNG/DAHIRU

28/08/2026

by
Masjid Abihuraira
(tooltip)Only people who manage this Page can see who published
·
7 minutes ago
·
Shared with Public
Kaitseye daga
khudubar sallan jumma'a
Daga Masallacin Abu Hurairah Dake Yan Tumatur Dei-DEI Abuja.
Imam Mahmud Sani Albany
15/03/1448 AH = 28/08/2026 AD See less

28/08/2026
28/08/2026

Kaitseye daga

Masallacin Abubakar Sadiq Masjid
dake airport road Lugbe Abuja.

Imam Abubakar Abdullahi yelwa ke gabatar da khudubar sallan jumma'a.

15/03/1448 AH = 28/08/2026 AD

28/08/2026

🤦🏻‍♂️Nasihohi (40) Dan Gyaran Gidajen Mu ⛪كتاب أربعون نصيحة من إصلاح البيوت 📖 Da Littafin Qawa'idul Fiqhu و كتاب قواعد الفقه📕Daga Majalisin Markazu Riyadhil Jannah📚

Tare Da:-👇

Sheikh Harith Jibreel Muhammad Abu Hamnah

🙋 Ayanzu Hakama Ana Kallan Malam A YouTube Channel Din:-👇

Tafarkin Magabata Tv🖥️

💁 Hardama Shafin Mu Na Tiktok Media:-👇

Tafarkin Magabata

A Safiyar Yau Jumma'a 15ga Watan Rabi'ul Awwal 1448H/28/8/2026

Tafarkin Magabata Media Director

28/08/2026

🙋🏻‍♂️Tafsirin Al-qur'aani Mai Girma📕 Acikin Suratuz-Zukhruf 📖تفسير القرآن الکريم في السورة الجاثية📚

Daga Bakin:-👇

Sheikh Muhammad Sani Sulaiman (As-sahabah)

Da Kuma:-👇

Al-hafiz Alh Nura Ibraheem Dan Kakalo Askolaye Kaduna

Ayau Jumma'a 15ga Watan Rabiu'ul Awwal 1448H/28/8/2026 Daga Masjidul Awwabin Askolaye Kaduna

Tafarkin Magabata Media Director

KUNGIYAR MATASA MASU DA'AWA NA SOCIAL MEDIA (DIYNET) TA CIKA SHEKARA 1 DA KAFAWAWannan kungiya mai suna a sama tayi Zama...
27/08/2026

KUNGIYAR MATASA MASU DA'AWA NA SOCIAL MEDIA (DIYNET) TA CIKA SHEKARA 1 DA KAFAWA

Wannan kungiya mai suna a sama tayi Zama na farko bayan cikar ta shekara ɗaya da kafawa,
Wannan ƙungiyar mai Albarka tayi wannan zaman ne a ranar Alhamis 27/8/2026

A yayin wannan zama Shugaban kungiyar Shaikh Ismail Ibrahim Danmalam Funtua

Yayi maraba da mahalarta taron, ya Kuma nuna jin daɗinsa irin yanda Membobin kungiyar ke Amsa gayyatar taron duk da irin uzurorin rayuwa da ake ciki,

Sannan Ya gabatar da Ta'aziyyar rasuwar ɗaya daga cikin Membobin wannan ƙungiyar Jajirtacce mai kokari wanda da Shawararshi da jajircewarshi ne aka kafa wannan kungiya Wato Shaikh Abdurrasheed M Surajo
Wanda Kafin rasuwarsa shine sakataren wannan ƙungiyar tun bayan kafuwar ta,

Shugaban ƙungiyar Shaikh Danmalam yayi Addu'ar samun rahama ga mamacin da fatan dukkanin mahalartan zasuyi koyi da irin halayensa da jajircewarsa a dukkanin abinda ya shafi Addini da Al'ummah,

A nashi jawabin sakataren tsare-tsare na ƙungiyar Malam Auwal Abdullahi A madadin mataimakin sakataren kungiyar malam Ibrahim Mu'azzam
Ya karanto wasu daga cikin zaman da akayi a baya,
Wanda zuwa yanzu anyi zama sama da sau 8 ƙarƙashin wannan ƙungiyar,

Sannan ya ƙara nanata karanta Manufofin wannan kungiya Mai albarka saboda sabbin membobi da s**a zo Daga baya, ya jaddada manufofin ƙungiyar Kamar haka;

1- FITO DA MARTABAR MALAMAI A IDANUN AL'UMMAH

2- HAƊIN KAN MATASA MASU DA'AWAH

3- NEMAWA AL'UMMAH MAFITA TA ADDINI DA RAYUWA

4- WAYAR DA KAN MATASA DON CIN GAJIYAR DAMAR DA ALLAH YA BA SU TA HANYAR GANE SU DIN SU WAYE!

5- INGANTA RAYUWAR MATA, ƘANANAN YARA DA MASU RAUNI,

Haka zalika dai Shugaban wannan ƙungiyar Malam Danmalam ya gabatar da jawabin makasudin wannan taro na yau,

Inda a cikin jawabin nasa ya zayyano nasarar da wannan ƙungiyar ta samu tun bayan kafuwar ta,
Wanda an Kafa ta ne a ranar; 17/July/2025

Anyi mata rijistar da gwamnatin jihar Katsina a ranar; 4/August/2025 kamar yanda yake rubuce a certificate din kungiyar,
Wanda hakan yasa ta cika shekara ɗaya da kafawa,

Shaikh Danmalam ya ƙara da cewa:
Daga wannan lokacin okacin da aka kafa ta zuwa yanzu an sami nasarori masu yawa,
Basu iya faduwa a yanzu,
Amma kaɗan daga cikin nasarorin Sun haɗa da;

1- Tara kuɗaɗe daga membobin ƙungiyar wanda ya bada damar aiwatar da ayyukan kungiyar dama tallafawa ba tare da neman taimakon kowa ba,

2- Nemawa Ƴan uwa musulmi wani muhimmin haƙƙi da kuma zakulo wata danniya da aka rinƙa yi masu a inda sune s**afi rinjaye kuma aka sami nasarar maganin matsalar cikin ikon Allah,

3- Shiga dumu-dumu wajen nemawa yara mahaddata Alqur'ani yanda zasu sami damar Samun tallafin karatun lafiya daga gwamnatin jihar Katsina,
Wanda hakan ya kaiga samun nasarar rubuta wasiƙa ta kai tsaye har zuwa wajen Gwamnan jihar Katsina,
Kamar yanda zaku iya ganin kwafin takardar a ƙasa,

4- Nemawa Wata baiwar Allah Tallafin ɗaukar nauyin rashin lafiya daga Shugaban Kungiyar Izalah ta ƙasa Shaikh Abdullahi Bala Lau,
Inda nan take ya dauki nauyin rashin lafiyar ta ko nawa za'a kashe (Duk da dai bayan tuntubar mara lafiyar mun samu wata ta fara tura deposit na 2millions na aikin)
Kuma shugaban ya tabbatar da cewa a shirye yake ya ɗauki nauyin rashin lafiyar duk inda za'a je,

5- Akwai wani muhimmin Albishir na taimakawa ga wani mara lafiya shima dake cikin Wani mawuyacin hali nan bada jimawa ba Insha Allah,

Waɗannan dama wasu nasarorin masu yawa duk suna cikin jawaban da shugaban kungiyar yayi a yayin wannan taron,

Kuma ya ƙara tabbatar da cewa wannan kaɗan kenan na abubuwan Alkhairi da ƙungiyar tayi bayan kafuwar ta shekara ɗaya zuwa yanzu,

Abubuwan da ƙungiyar zata tunkara nan gaba ana sa ran zasu fi girmama, watsuwa da yaɗuwa da iznin Allah,

Sannan kuma har yanzu Kofar wannan kungiya buɗe take ga dukkanin sabbin membobin dake sha'awar shiga domin bada tasu gudunmawa ga Addini da Al'ummah,

A nasu jawaban!
Dukkanin mahalarta taron sun nuna jin daɗinsu game da wannan kungiya da irin nasarorin da ƙungiyar ta samu,

Sun kuma buƙaci da a kara tashi ayi aiki tukuru ba tare da kasala da gajiyawa ba domin haɓɓaka addini da samawa al'umma mafita,

Daga karshe dai an rufe wannan taron,
Kuma an saka ranar Zama na gaba In Allah ya kaimu,

✍️
Rahoto daga
Jami'in Hulda da jama'a na ƙungiyar
ta hannun
Sakataren kafofin sadarwa na zamani
Nasiru Sulaiman Funtua

ALHAMDULILLAH 🥹🙏Cikin hukuncin uban gijiAnyima Zainab sunusi aiki na farko saura aiki na biyu (2)Don Allah kuci gaba da ...
27/08/2026

ALHAMDULILLAH 🥹🙏
Cikin hukuncin uban giji
Anyima Zainab sunusi aiki na farko saura aiki na biyu (2)

Don Allah kuci gaba da bibiya ta Musan Baba
Domin kuga wakilcin da kuka bani
Da amanar ku🥹🙏

Kunesila foundation 🥹♥️🙏

Address

Unguwar Dahiru, Sokoto Road
Funtua
830101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Funtua Islamic Channel posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Funtua Islamic Channel:

Shortcuts

Share