Darul Islam

Darul Islam من جآء بالحسنةفله عشر أمثالها

19/02/2026

Ramadan Tafsir Day 001 Sheikh Shafi,u halliru Dabai and Ustaz Aminu Muhammad Dabai.

Tahfizul Qur,an watarbiyyatul Aulad Dabai

12/09/2024
09/07/2024



Assalamu Alaikum Warahmatullah





Goma ga watan Almuharram itache ranar Ashurah akwai muhimman abubuwa da tarihi ya kiyaye cewar sun faru a wannan ranar.

Amma dai wanda yafi taɓamu kai tsaye shine shahadar da jikan ma'aiki Sallallahu alaihi Wasallama kuma shugaban matasan aljannah yayi Al-imamu Husaini Radiyallahu Anhu a wannan ranar ta ashurah.

Koh shakka babu dukkanin ɗaukachin Ahlu-sunnah suna da fahimtar cewar An kashe sayyiduna Al-husain ne matsayin Wanda aka zalunta.

Sai dai Akwai bukatar mu fahimci wasu abubuwa guda goma 10 wanda dukkansu suna da alaƙa da shahadar sayyiduna Husaini Radiyallahu Anhu, kuma wanda ya jahilce su bai kamata ya tsoma baki akan qadiyyar ba.

1. Kafin Ya fita domin zuwa Wajen da yayi shahada yana ina ne da Zama ?

2. Shin Sahabbai da sauran Ahlul-baiti sun goyi bayan ya fita zuwa inda yayi shahada Koh sun tsawatar mishi akan haka. ?

3. Shin su wanene acikin tawagar shi lokacin da ya fita domin dai bashi kaɗai bane.

4. Menene sababbin fitar shi zuwa inda yayi shahada ? Sanin wannan yanada muhimmanci

5. Shin sayyiduna Husaini shi kaɗai ne yayi shahada Koh akwai wasu Tare Da shi awannan lokacin da suma s**a yi shahadar, amma dayawan musulmi basa jin sunan su

6. Su wanene s**a gayyato shi inda yayi wannan shahadar, shin sun taimaka mishi da ya iso Wajen, koh gadar zare su kayi mishi ?

7. Su wanene s**a kashe shi kuma ƙarƙashin jagorancin wanene

8. Menene matsayar Yazidu ɗan Mu'awiyah akan wannan mas'alar awajen sauran Musulmi

9. Shin wace wasiyya sayyiduna Husaini yayi ma ƴar-uwar shi zainab kafin yayi shahada, shin Mabiya addinin shi'ah suna kula da wannan wasiyyar Koh kuwa ?

10. Menene tarihin masu zanga-zanga da kuka da shiga Bala'i a dukkanin lokacin da irin wannan rana ta zagayo, wadda al'imam Husaini yayi shahada ?

Mu hadu a rubutun da suke biye domin yin ƙarin haske akan wannan in Sha Allahu

Engr Aliyu Nasir Sambo-ja

10/03/2024

ALBISHIRIN AL-UMMAR MUSULMI DAGA KO'INA A FADIN DUNIYA.

wannan page na DARUL ISLAM na sanar da ku cewa: zata Dunga kawo maku tafseer Ramadan Kai tsaye daga masallacin asibiti Dabai (phc,Dabai)

Wanda Mal. Auwal Tukur zai riƙa gabatarwa insha Allah

Ku kasance da DARUL ISLAM gobe Litini da karfe 4:30pm domin kallon shirin kai tsaye, in sha Allah.

03/03/2024

Darasi Na (04) Akan Azumi.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
(Hukuncin Sahur Da Falalarsa Part One)

Ma'anar:
✍️Sahur Shine Abuncinda Ake Ci Kafin Fitowar Alfijir Na Biyu Bayan Fitowar Alfijir Na Farko .

Hukuncin Sa:
✍️Malamai Dadama Sun Tafi Akan Cewar Sahur Wajibi Ne Duba Da Wannan Hadisi.
عن أنس بن مالك - رضي الله عنه - قال: قال رسول اللَّه - صلى الله عليه وسلم - «تَسَحَّرُوا، فَإِنَّ فِي السَّحُورِ بَرَكَةً».
〈حكم الحديث : متفق عليه〉

Kamar Yanda Kuka Gani Anas Bin Malik Yana Cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace:

(Kuyi Sahur Domin Acikin Sahur Akwai Albarka)

Kunga A Zahari Manzon Allah Sallallahu Alaihi Umarni Yayi Cewar Kuyi Sahur Kunga Umarnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ana Daukarsa Wajibi Sai Idan Akwai Dalilinda Ke Nuna Ba Wajibi Bane.

👉Amma Kasantuwar An Samu Ya Taba Hade Azumin Kwanaki Dadama Ajeri Ba Tareda Sahur Ko Buda Baki Ba Sai Aka Gano Cewar Shi Sahur Ba Wajibi Bane Saidai Sunnah Ce Mai Karfin Gaske.

✍️Kuma Abunda Sunnah Ta Tanadar Shine A Jinkirta Sahur Kuma Bidi'a Ne Sanya Wani Lokaci Na Rufe Sahur Matukar Ba Lokacin Fitowar Alfijir Bane.

13/02/2024

Duk Wanda yayarda Allah shine ubangijin shi Musulince Shine Addinin Shi Annabi Muhammad SAW shine ma
nzan shi

Haqiqa Imanin shi yacika

Dadin Duniya Mai karewa
13/02/2024

Dadin Duniya Mai karewa

26/01/2024

Hadith Ya inganta daga abihurairata Allah yakara yarda dashi ya ce

Manzan Allah tsirada amincin Allah s**ara tabbabata agrashi ya ce

KALMOMI GUDA BIYU

masu saukin fidi akan harshe
masu nauyi akan sikeli
masu soyuwa agurin Allah

SUNE

SUBHAANALLAHI
WALHAMDULLAHI

(Bukhai da Muslim)

03/01/2024

IDAN MUKAZO KWANCIYA BARCI
Mu yafewa kowa sannan mu nemi yafiyar Allah (swt) ga dukkanin zunabanmu da s**a gabata.
Domin waninmu idan ya kwanta ba zai iya tashi ba
Mu nema yafiyar zunabanmu damu muka aikata Allah zai yafe mana,
Allah ya gafarta mana dukkanin zunabanmu wadanda muka sani da wadanda ma bamu sani ba

DAGA CIKIN FALALAR KARANTA ALQUR'ANI MAI GIRMA              Manzon Allah tsira da Amincin Allah su qara tabbata agareshi...
02/01/2024

DAGA CIKIN FALALAR KARANTA ALQUR'ANI MAI GIRMA

Manzon Allah tsira da Amincin Allah su qara tabbata agareshi yace

Wanda yake karanta alqur'ani har ya zama gwani ko ya kware a karatun to yana tareda mala'iku masu daraja.

Wanda kuma yake koyan karatun Qur'ani, yake ta* *maimitawa ko yake ta tuntube a lokacin da yake karatun, yana shan wahala, to yanada lada biyu.

*Ma'ana, Allah zai ninka masa ladan karatun alqur'ani da yakeyi.

عَنْ عائشةَ رَضِيَ اللهُ عنْهَا قالتْ: قال رسولُ اللهِ ِ صَلّى اللهُ عَلَيْهِ وسَلَّم:
"الَّذِي يَقرَأُ القُرْآنَ وَهُوَ ماهِرٌ بِهِ.. معَ السَّفَرةِ الكرَامِ البررَةِ، والَّذِي يقرَأُ القُرْآنَ ويتَتَعْتَعُ فِيهِ وَهُوَ عَليْهِ شَاقٌّ.. لهُ أجْرانِ"
(مُتَّفَقٌ عَلَيْه)
Saboda haka kada mutum ya gaji da koyon karatun alqur'ani Mai girma a kowane lokaci.

17/12/2023

NANA ZAINAB BINT JAHSH RA (1)

"زوجكن اهاليكن وزوجني الله تعالى من فوق سبع سموات"

NASABARTA DA AURENTA DA ANNABI (SAW)

Nana Zainab bint Jahsh رضى الله عنها وأرضاها ita ce, Zainab 'yar Jahsh dan Ri'bàb dan Ya'amur Al-Asadiyya. Mahaifiyarta ita ce: Umaimah bint Abdulmuddalib, gwaggon Annabi صلى الله عليه وسلم 'yar'uwar mahaifinsa, kuma 'yar'uwar Hamza bn Abdulmuddalib رضى الله عنه baffan Annabi صلى الله عليه وسلم. Saboda haka ita kanwa ce ga Annabi صلى الله عليه وسلم.

Nana Zainab matashiya ce kyakkyawa, 'yar madaukakin dangi na kuraishawa, jikar Abdulmuddalib kakan Annabi صلى الله عليه وسلم.

Mijinta na fari shi ne Zaid bn Harith رضى الله عنه. Annabi صلى الله عليه وسلم ya riki Zaid kamar dansa har ma ana kiransa Zaid bn Muhammad, har sai da Allah سبحانه وتعالى ya hana a danganta kowa in ba ga mahaifinsa ba, shi ne aka dawo ana kiransa da Zaid bn Harith.

Annabi صلى الله عليه وسلم yana matukar kaunar Zaid, har ma ana kiransa dan lelen Manzon Allah صلى الله عليه وسلم. Da Zaid ya isa aure sai Annabi صلى الله عليه وسلم ya aura masa kanwarsa Zainab bint Jahsh. Ya zauna da ita tsawon shekara guda, amma zaman nasu bai yi dadi ba saboda tana ganinta karkashin bawa duk da cewa Annabi صلى الله عليه وسلم ya 'yanta shi, ita kuma ga ta da nasaba madaukakiya ta kuraishawa. Zaid sai ya rika kai kararta wajen Annabi صلى الله عليه وسلم, shi kuwa yana lallashinsa yana fada masa cewa ya ji tsoron Allah ya rike matarsa.

Larabawa a lokacin jahiliyya sun yarda cewa idan mutum yana rikon wani a matsayin dansa, to haramun ne a kansa ya auri matar da ya saki domin a wurinsu kamar ya auri matar dan da ya haifa ne bayan ya sake ta.

To da yake Allah سبحانه وتعالى ya yi nufin rushe waccan al'ada ta jahiliyya dongane da ya'yan riko wadanda ba daidai suke da ya'yan cikin mutum ba sai ya sanar da Manzonsa cewa Zaid zai saki matarsa Zainab shi kuma zai aureta bisa umarnin Allah سبحانه وتعالى.

Da zama ya ki yiwuwa tsakanin Zaid da matarsa Zainab sai ya sake ta.

Anas رضى الله عنه ya

Address

Dabai
Danja

Telephone

+2348125459039

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Darul Islam posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share