09/07/2024
Assalamu Alaikum Warahmatullah
Goma ga watan Almuharram itache ranar Ashurah akwai muhimman abubuwa da tarihi ya kiyaye cewar sun faru a wannan ranar.
Amma dai wanda yafi taɓamu kai tsaye shine shahadar da jikan ma'aiki Sallallahu alaihi Wasallama kuma shugaban matasan aljannah yayi Al-imamu Husaini Radiyallahu Anhu a wannan ranar ta ashurah.
Koh shakka babu dukkanin ɗaukachin Ahlu-sunnah suna da fahimtar cewar An kashe sayyiduna Al-husain ne matsayin Wanda aka zalunta.
Sai dai Akwai bukatar mu fahimci wasu abubuwa guda goma 10 wanda dukkansu suna da alaƙa da shahadar sayyiduna Husaini Radiyallahu Anhu, kuma wanda ya jahilce su bai kamata ya tsoma baki akan qadiyyar ba.
1. Kafin Ya fita domin zuwa Wajen da yayi shahada yana ina ne da Zama ?
2. Shin Sahabbai da sauran Ahlul-baiti sun goyi bayan ya fita zuwa inda yayi shahada Koh sun tsawatar mishi akan haka. ?
3. Shin su wanene acikin tawagar shi lokacin da ya fita domin dai bashi kaɗai bane.
4. Menene sababbin fitar shi zuwa inda yayi shahada ? Sanin wannan yanada muhimmanci
5. Shin sayyiduna Husaini shi kaɗai ne yayi shahada Koh akwai wasu Tare Da shi awannan lokacin da suma s**a yi shahadar, amma dayawan musulmi basa jin sunan su
6. Su wanene s**a gayyato shi inda yayi wannan shahadar, shin sun taimaka mishi da ya iso Wajen, koh gadar zare su kayi mishi ?
7. Su wanene s**a kashe shi kuma ƙarƙashin jagorancin wanene
8. Menene matsayar Yazidu ɗan Mu'awiyah akan wannan mas'alar awajen sauran Musulmi
9. Shin wace wasiyya sayyiduna Husaini yayi ma ƴar-uwar shi zainab kafin yayi shahada, shin Mabiya addinin shi'ah suna kula da wannan wasiyyar Koh kuwa ?
10. Menene tarihin masu zanga-zanga da kuka da shiga Bala'i a dukkanin lokacin da irin wannan rana ta zagayo, wadda al'imam Husaini yayi shahada ?
Mu hadu a rubutun da suke biye domin yin ƙarin haske akan wannan in Sha Allahu
Engr Aliyu Nasir Sambo-ja