10/06/2026
🌿 Daga Cikin Fa’idojin Addu’ar Bayan Kiran Sallah 🌿.
Wannan addu’a tana daga cikin manyan addu’o’in da Manzon Allah ﷺ ya koyar da al’ummarsa su rika yi bayan an gama kiran sallah. A cikinta akwai salati ga Annabi ﷺ da kuma rokon Allah Ya ba shi matsayi mafi girma da daraja mafi ɗaukaka a Aljanna. Wannan yana nuna girman matsayin Annabi Muhammad ﷺ da kuma muhimmancin ƙaunarsa a zuciyar ki wane Musulmi.
Haka kuma wannan addu’a tana koyar da mumini ya kasance mai bin Sunnah da kuma amfani da lokutan da ake amsa addu’a. Bayan kiran sallah lokaci ne mai albarka, don haka Musulmi yana amfani da wannan dama wajen kusantar Allah da neman yardarsa ta hanyar bin abin da Annabi ﷺ ya koyar.
A cikin hadisi sahihi, Manzon Allah ﷺ ya bayyana cewa duk wanda ya fadi wannan addu’a bayan ya ji kiran sallah, zai cancanci cetonsa da shafa’arsa a ranar Alƙiyama. Wannan falala ce mai girma da ya kamata Musulmi ya yi ƙoƙarin samu ta hanyar kiyaye wannan Sunnah a ko wane lukacin da aka kira salla.
Ku kasance da shafin mu na * Da'awah a kafafen sada zumunta Da kuma Shafina Habeeb* domin cigaba da samun waɗannan Addo'o'in da zikirori Ingantattu in Sha Allah daga cikin littafin Hisnul Muslim
✍️ Ahlulkhair Da’awah
* *
* *
https://whatsapp.com/channel/0029Vb7Kw88CXC3CYDUFdz1A