29/05/2026
Wadannan mutanen sun dauki aikin Hajji kamar “content creation trip” ne fah 🤣
Ba ka gama ganin su a Mina ba sai ka sake ganin su a status:
“Alhamdulillah muna kan hanyar Jamarat 🤳”
Anan kuma wani na can yana ta kuka yana neman gafarar Allah, su kuwa suna neman angle mai kyau da filter 😭
Wallahi akwai mutanen da idan s**a je Hajji, Shaiɗan ma sai ya rasa shin ibada s**a zo yi ko documentary? Duk inda s**a tsaya sai:
🎥 “Assalamu alaikum followers dina yanzu muna kofar hotel...”
🎥 “Ga abincin breakfast din Hajji... 🤣”
🎥 “Ga lokacin da nake shiga lif din Harami...” 😂
Kai har Ka’aba bata da privacy a hannunsu 😭
Allah Maɗaukakin Sarki yace:
﴿فَمَن كَانَ يَرْجُو لِقَاءَ رَبِّهِۦ فَلْيَعْمَلْ عَمَلًا صَـٰلِحًۭا وَلَا يُشْرِكْ بِعِبَادَةِ رَبِّهِۦٓ أَحَدًۭا﴾
Ma’ana: Duk wanda yake fatan haɗuwa da Ubangijinsa, to ya aikata aiki na gari kuma kada ya haɗa kowa cikin ibadar Ubangijinsa.
Amma su wadannan idan basu nuna maka cewa sunyi Hajji ba, kamar Hajjin bai kai server ɗin sama ba
Sai ka ga mutum yana dawafi amma zuciyarsa tana duba comments:
Annabi ﷺ yace:
«إِنَّ أَخْوَفَ مَا أَخَافُ عَلَيْكُمُ الشِّرْكُ الْأَصْغَرُ»
قَالُوا: وَمَا الشِّرْكُ الْأَصْغَرُ يَا رَسُولَ اللَّهِ؟
قَالَ: «الرِّيَاءُ»
Ma’ana: “Abin da na fi tsorata muku shi ne ƙaramin shirk.”
Sai aka ce: “Menene shi?”
Yace: “Riya.”
Mai tsoron ALLAH na gaskiya idan yayi ibada yana ƙoƙarin ɓoye ta.
Amma ‘yan kwaram kuwa idan s**a shiga Harami, camera ce ke shiga kafin su 😀
Wasu ma sai ka rantse idan babu data a Saudiyya da rabinsu basu zuwa Hajji 😂
Hajji ba fashion week bane.
Ba reality show bane.
Ba “update your status every 5 minutes” bane.
Hajji wajen:
🕋 tuba ne
🕋 hawaye ne
🕋 tsoron Allah ne
🕋 karya kai ne
ٱلْحَجُّ أَشْهُرٌ مَّعْلُومَاتٌ ۚ فَمَن فَرَضَ فِيهِنَّ ٱلْحَجَّ فَلَا رَفَثَ وَلَا فُسُوقَ وَلَا جِدَالَ فِى ٱلْحَجِّ ۗ وَمَا تَفْعَلُوا۟ مِنْ خَيْرٍ يَعْلَمْهُ ٱللَّهُ ۗ وَتَزَوَّدُوا۟ فَإِنَّ خَيْرَ ٱلزَّادِ ٱلتَّقْوَىٰ ۚ وَٱتَّقُونِ يَـٰٓأُو۟لِى ٱلْأَلْبَـٰبِ
Ma’anarta Ayar
Hajji yana cikin watanni sanannu. Wanda ya ɗauki niyyar yin Hajji a cikinsu, to babu jima’i, babu saɓo, babu jayayya a lokacin Hajji. Kuma duk abin alkhairi da kuka aikata, Allah Ya san shi. Kuma ku yi guzuri, domin mafi alherin guzuri shi ne taƙawa. Kuma ku ji tsorona, ya ma’abota hankali