24/08/2026
*LITININ, 24 GA AGUSTA*
*NASSI: WAHAYIN YAHAYA 19:11-21*
*KAN MAGANA: MAHAYIN FARIN DOKI: YAKIN ARMAGEDDON*
*WAHAYIN YAHAYA 19:11-21*
11: Sai na ga sama ta dāre, sai ga wani farin doki! Mahayinsa kuwa ana ce da shi Amintacce, Mai Gaskiya, yana hukunci da adalci, yana kuma yaƙi.
12: Idanunsa k**ar harshen wuta suke, kansa da kambi da yawa, yana kuma da wani suna a rubuce, wanda ba wanda ya sani sai shi.
13: Yana saye da riga wadda aka tsoma a jini, sunan da ake kiransa da shi kuma, shi ne Kalman Allah.
14: Rundunonin Sama, saye da lallausan lilin fari mai tsabta, suna a biye da shi a kan fararen dawakai.
15: Daga cikin bakinsa wani kakkaifan takobi yake fitowa, wanda zai sare al'ummai da shi, zai kuwa mallake su da tsanani ƙwarai, zai tattake mamatsar inabi, ta tsananin fushin Allah Maɗaukaki.
16: Da wani suna a rubuce a jikin rigarsa, har daidai cinyarsa, wato Sarkin sarakuna, Ubangijin iyayengiji.
17: Sa'an nan na ga wani mala'ika tsaye a jikin rana. Sai kuma ya kira dukkan tsuntsaye da suke tashi a sararin sama, da murya mai ƙarfi, ya ce, “Ku zo, ku taru wurin babban bikin nan na Allah,
18: ku ci naman sarakuna, da naman sarakunan yaƙi, da naman ƙarfafa, da naman dawakai, da na mahayansu, da naman kowa da kowa, wato, na ɗa da na bawa, na yaro da na babba.”
19: Sai na ga dabbar nan, da sarakunan duniya, da rundunoninsu, sun taru, don su yaƙi wanda yake kan dokin, da kuma rundunarsa.
20: Sai aka k**a dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda s**a yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda s**a yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.
21: Sauran kuwa aka sare su da takobin wanda yake a kan doki, wato, da takobin nan da yake fitowa daga cikin bakinsa. Dukan tsuntsaye kuwa s**a ci namansu har s**a yi gamba.
*MAHAYIN FARIN DOKI: YAKIN ARMAGEDDON*
Yahaya ya bayyana mana abin da gani sa’ad da Sama ta bude, kuma Farin Doki da mahayinsa wanda bayyaninsa ke dauke da lakabin cewa Yesu ne kadai ya cancanci daukaka, aya 11-14.
A cikin ayarinsa akwai sojoji daga sama, kuma suna kan fararen dawakai, suna sanye da lallausan lilin, fari mai tsabta. Karin Wahayi game da mahayin shine, daga bakinsa takobi mai kaifi na fitowa, wanda da ita zai kashe al’ummai.
Yadda abubuwan suke sun nuna cewa mahayin bai zo don zaman lafiya ba, k**ar yadda yake a farkon zuwansa, amma don yaki. Ya kuma shirya ya mallaki duniya da sandar karfe, ya sa a rubuta wannan suna a dukan rigarsa da cinyoyinsa, “SARKIN SARAKUNA DA UBANGIJIN IYAYENGIJI.”
Da wadannan ne aka shirya fagen yaki, a gefe guda kuma akwai namomin jeji, da sarakunan duniya, da rundunarsu, s**a taru domin yaki da mahayin doki da rundunarsa.
Wannan shine Babban Yakin Armageddon inda dabbar da dukan aljannunsa za su hadu da hallakarsu aya 15-21, daga nan sai mulkin na karni ya biyo baya.
*TAMBAYA:* Menene ya k**ata mu yi da sanannen Sarkin Sarakuna kuma Ubangijin Iyayengiji?
*ADDU’A:* Ubangiji Yesu, ina addu’a cewa zukatan sarakunan duniya su narke kuma su fara rayuwa cikin adalci sabili da Almasihu. Amin.
*Abincin Yini - 2026*