Daru Ahlil Qur'an

Daru Ahlil Qur'an Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Daru Ahlil Qur'an, Religious organisation, Anchau.

وَكَذَلِكَ أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ رُوحًا مِنْ أَمْرِنَا مَا كُنتَ تَدْرِي مَا الْكِتَابُ وَلَا الْإِيمَانُ وَلَكِن جَعَلْنَاهُ نُورًا نَّهْدِي بِهِ مَن نَّشَاءُ مِنْ عِبَادِنَا وَإِنَّكَ لَتَهْدِي إِلَى صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ صِرَاطِ اللَّهِ الَّذِي لَهُ مَا

001 Masha Allah Allah yakara lfy gwaniMAI MARTABA SARKIN ZAZZAU YA KARRAMA ALARAMMA ABUBAKAR UMAR BALARABEA Fadansa dake...
20/04/2026

001 Masha Allah Allah yakara lfy gwani

MAI MARTABA SARKIN ZAZZAU YA KARRAMA ALARAMMA ABUBAKAR UMAR BALARABE

A Fadansa dake Birnin Zariya, a jiya Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR, ya karrama Alaramma Abubakar Umar Balarabe.

Haifafen Garin Zariya. Alaramma Abubakar wanda yai karanta Kimiyyan Na'u'ra mai Kwakwalwa a Jami'ar Madina ya sami amincewa da sheda daga Manyan Limaman Kasar Saudiya na ya karanta Al'kurani mai cikin Kiran Warsh a kowane bangare na Duniya wanda Mai Martaba Sarkin Zazzau ya karramashi tare da kaddamar da Kaset din karatun sa da kuma umurtan al'umma da su fashion kofensa domin amfaninsu.

Daru Ahlil Qur'an......✍️

001 SHAWARA GAMASU SON HADDACE AL QUR'ANI MAI GIRMA 👇👇👇👇👇👇1. Gyara niyya da fahimtar buriKa tabbata kana yi don neman ya...
20/04/2026

001 SHAWARA GAMASU SON HADDACE AL QUR'ANI MAI GIRMA 👇👇👇👇👇👇

1. Gyara niyya da fahimtar buri
Ka tabbata kana yi don neman yardar Allah, ba don yabo ba. Wannan yana taimaka maka ka daure idan wahala ta zo.
2. Zaɓi lokaci mafi dacewa
Mafi inganci:
Bayan Asuba
Ko da dare kafin ka kwanta
A wannan lokaci kwakwalwa tana da nutsuwa.
3. Ƙananan aya amma da inganci
Kar ka yi gaggawar ɗaukar yawa:
Aya 3–5 a rana sun isa (idan kai beginner ne)
Ka karanta su sau 10–20 kafin ka fara haddacewa
Sannan ka maimaita ba tare da dubawa ba
4. Maimaitawa shi ne sirri
Haddacewa ba tare da maimaitawa ba = mantuwa. Ka raba lokacinka:
Sabon haddacewa
Maimaita tsohon (wannan ya fi muhimmanci ma)
Misali:
Sabo: minti 20
Maimaitawa: minti 40
5. Ka haɗa haddacewa da sallah
Ka riƙa karanta abin da ka haddace a cikin sallah
Wannan yana ƙarfafa ƙwaƙwalwa sosai
6. Ka sami malami ko abokin gyara
Ko da kana iya karantawa:
Malami zai gyara maka tajwidi
Zai hana ka haddace kuskure
7. Fahimtar ma’ana
Kar ka haddace kawai:
Ka karanta fassara
Idan ka fahimta, zai fi sauƙin haddacewa
8. Tsari na mako
Ka yi shiri kamar haka:
Kullum: sabo + maimaitawa
Karshen mako: ka maimaita duk abin da ka haddace
9. Haƙuri da juriya
Gaskiya: za ka manta wani lokaci. Wannan ba alama ce ka kasa ba—al’ada ce. Abin da ya fi muhimmanci shi ne ka dawo ka ci gaba.
Matakin da mutum zai bi (summary):
Niyya mai kyau
Zaɓin lokaci mai kyau
Ƙananan aya a rana
Maimaitawa sosai
Amfani da sallah
Samun malami
Fahimtar ma’ana
Tsari na mako
Haƙuri

Allah Yabamu SA'A Ameen 🤲

Daru Ahlil Qur'an........✍️

20/04/2026

Allah yara ka/ki sama da shekara {10} aduniya saunawa kataba Karanta Al Qur'ani bango suwa bango tambayyi kan ka/ki🤔

20/04/2026

001Masha Allah

gwani Usman Wadata from kaduna state
Daru Ahlil Qur'an

001 Masha Allah Result ya Fito kusanyamasa Al Barka Gwani Usman wadata Kaduna State Nigeria🇳🇬yazo na Biyar a gasan Al Qu...
20/04/2026

001 Masha Allah Result ya Fito kusanyamasa Al Barka

Gwani Usman wadata
Kaduna State Nigeria🇳🇬

yazo na Biyar a gasan Al Qur'ani da agabatar Na online Daru Ahlil Qur'an

kukasance tare damu Wani Sati Raman Jumma'a Allah yakaimu lokaci ameen🤲

001 Masha Allah Result ya Fito kusanyamasa Al Barka Gwani Abdulsalam Ahmad (Kiri)Jigawa State Nigeria🇳🇬yazo na Na hudu a...
20/04/2026

001 Masha Allah Result ya Fito kusanyamasa Al Barka

Gwani Abdulsalam Ahmad (Kiri)
Jigawa State Nigeria🇳🇬

yazo na Na hudu a gasan Al Qur'ani da agabatar Na online Daru Ahlil Qur'an

kukasance tare damu Wani Sati Raman Jumma'a Allah yakaimu lokaci ameen🤲

001 Masha Allah Result ya Fito kusanyamata Al Barka  Gwana Ummu Muhsin (Bintu salis) Taraba  State Nigeria🇳🇬tazo ta ta u...
20/04/2026

001 Masha Allah Result ya Fito kusanyamata Al Barka

Gwana Ummu Muhsin (Bintu salis)
Taraba State Nigeria🇳🇬

tazo ta ta uku a gasan Al Qur'ani da agabatar Na onlinDaru Ahlil Qur'anan

kukasance tare damu Wani Sati Raman Jumma'a Allah yakaimu lokaci ameen🤲

001 Masha Allah Result ya Fito kusanyamata Al Barka Gwana Maryam Abubakar zamfara State Nigeria🇳🇬tazo  ta biyu a gasan A...
20/04/2026

001 Masha Allah Result ya Fito kusanyamata Al Barka

Gwana Maryam Abubakar
zamfara State Nigeria🇳🇬

tazo ta biyu a gasan Al Qur'ani da agabatar Na onlinDaru Ahlil Qur'anan

kukasance tare damu Wani Sati Raman Jumma'a Allah yakaimu lokaci ameen🤲

001 Masha Allah Result ya Fito kusanyamata Al Barka Gwana sumayyah Umar shiek Niger State Nigeria🇳🇬tazo ta ta farko a ga...
20/04/2026

001 Masha Allah Result ya Fito kusanyamata Al Barka

Gwana sumayyah Umar shiek
Niger State Nigeria🇳🇬

tazo ta ta farko a gasan Al Qur'ani da agabatar Na onlinDaru Ahlil Qur'anan

kukasance tare damu Wani Sati Raman Jumma'a Allah yakaimu lokaci ameen🤲

001M***i, Alƙali Murtadwa Nasir bai fara karantar da Bukhari da Muwaɗɗa ba tun (19s) sai da malaminsa ya ce ya karantar!...
20/04/2026

001M***i, Alƙali Murtadwa Nasir bai fara karantar da Bukhari da Muwaɗɗa ba tun (19s) sai da malaminsa ya ce ya karantar! Ɗan Kaduna ne mai yin abu da gaske, natsuwarsa ita kanta tana da natsuwa ta musamman ƙwarai da gaske. Ga tawali'u da kirki da mutuntawa! Matashi ne amma dottijo ne a karatu da mu'amala! ❤️

Bayan ya yi jami'ar Azhar, ya yi digiri na 2, kowa ya san yadda Azhar take da tsanani, Allah ya taimake shi ya wuce "Darul ifta" ta Misra wanda a can ake yaye duk wani mai fatawa! Bayan shekara da shekaru Alƙali Murtadwa ya yi nasara kuma wannan cibiya ta ba shi "Ijaza" don ya fara bayar da fatawa ko'ina a duniya.
Sai ka cancanta ka je wajen, tun safe ake fara karatu har bayan La'asar! Shekara da shekaru za ka yi kana bugawa daidai gwargwado!

Matashi ne amma ɗan baiwa, wasu ma in ba yanzu ba ba su san shi ba, cancantarsa ce ta sa babban M***i Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi s**a ga dacewar ya fara darasi na "Attargib-wattarhib" a Sultan Bello Mosque Kaduna kuma s**a sanya shi cikin makusantansu! Ya kasance ana gayyatar sa Africa Tv3 don bayar da fatawa kai-tsaye!

Malami ne wanda tun can asali mai karatu ne da bin malamai ba wai a sama ya ɗauki abin ba, lallai an ce malami shi ya san malami amma ko jahili mai natsuwa ya saurare shi zai gane da bambancin. Ina ƙwaɗaitar da jama'a a lizimi malam domin Allah ya ba shi baiwa da hikimar isar da saƙo. Ɓangaren ilimi kuma dama sha-kundum ne shi.

Ilimi ne ya haɗu da hikima da baiwa da natsuwa da samartaka da tarbiyya da ladabi da kuma sanin yakamata. Abin da da yawan malamai ba su cika haɗawa ba a wannan zamanin da muke ciki! Allah ya haɗa su ya tattara wa Imam, Alƙali Murtadwa!

Allah ƙara masa lafiya da iyayenmu, ya ƙara masa ikhlasi da iyayenmu🤲
Daru Ahlil Qur'ann......✍️

001 Masha Allah Result yafito Allah yasakama KOWA da KOWA da alkairi Allah ya amsa Abin da akaranta Ameen 🤲 DARU AHLIL Q...
20/04/2026

001 Masha Allah Result yafito Allah yasakama KOWA da KOWA da alkairi Allah ya amsa Abin da akaranta Ameen 🤲

DARU AHLIL QUR'AN ONLINE

CENTER FOR QUR'AN AND SUNNAH

Presents

COMMEMORATIVE POSTER OF SPECIAL RECITATION BY WINNING PARTICIPANTS OF THE NATIONAL MUSABAQAH

CONGRATULATIONS TO THE HAFIZ & HAFIZA RECITERS

WINNER RANKINGS & RESULTS

Daru Ahlil Qur'an......✍️

001 Masha Allah Abin ban Sha' awa 👇Musabaqa Sautiyya ta Yara ce zallah Present by Hafazatul Qur'an TvStay tuned for upda...
19/04/2026

001 Masha Allah Abin ban Sha' awa 👇
Musabaqa Sautiyya ta Yara ce zallah
Present by
Hafazatul Qur'an Tv
Stay tuned for update
Muhammad Makarfi Hall kinkinau Kaduna states Nigeria 🇳🇬
1 Day After Sallah
🌻🌼🌼🌻
Allah yakaimu lokacin Ameen 🤲

Daru Ahlil Qur'an.....✍️

Address

Anchau
2704

Website

https://www.facebook.com/profile.php?id=61583705524709, https://

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Daru Ahlil Qur'an posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share