23/05/2026
ABINCIN YINI NA ECWA
ASABAR, 23 GA MAYU
NASSI: AFISAWA 5:15-21
KAN MAGANA: TAFIYA CIKIN HIKIMA
AFISAWA 5:15-21
15. Saboda haka, sai ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai masu hikima.
16. Ku yi matuƙar amfani da lokaci don kwanaki mugaye ne.
17. Don haka kada ku zama marasa azanci, sai dai ku fahimci abin da yake nufin Ubangiji.
18. Kada kuma ku bugu da giya, hanyar masha'a ke nan. Sai dai ku cika da Ruhu,
19. kuna zance da junanku da kalmomin zabura, da waƙoƙin yabo, da waƙoƙi na ruhu, kuna raira waƙoƙi da zabura ga Ubangiji da yabo a zukatanku.
20. Kullum ku riƙa gode wa Allah Uba da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu a kan ko mene ne.
21. Ku bi juna saboda ganin girman Almasihu.
TAFIYA CIKIN HIKIMA
Yin koyi da Allah da yin rayuwa cikin Ubangiji Yesu Almasihu na bukatar hikima, wanda Bulus ya waiwaya gare shi a nassin yau.
Ka yi la’akari da yadda ya ce a cikin aya ta15-16: “Saboda haka sai ku maida hankali ga kwarai ga zamanku, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai masu hikima. Ku yi matukar anfani da lokaci don kwanakin mugaye ne.”
Amon muryar da aka yi anfani da shi a nan yana nuna muhimmanci da gaggawar abinda Bulus yake kiran Mai Bi zuwa gare shi.
Ka lura cewa ya kira Afisawa su “duba da kyau” yana nuna wajibcin, wanda aka kara nanata shi cikin hali “ba kamar marasa hikima ba, amma masu hikima.”
Ya bada dalilin irin wannan kira mai muhimmanci da cewar “domin kwanakin mugunta ne.”
Hanya daya da za a yi anfani da hikima a wadannan mugayen kwanaki ita ce ta fahimtar “menene nufin Ubangiji” da kuma “cika da Ruhu Mai Tsarki” (aya 17-18).
Sakamako shine rayuwa mai cike da farin ciki da yabo ga Allah, zama albarkar zaman tare, bautawa juna saboda girmamawa ga Almasihu, da kara darajar ga dukan mutanen da Allah ya kawo cikin rayuwar ka.
TAMBAYA:
Ta yaya ka san cewa hikimar Allah ce ke jagorantar rayuwarka?
ADDU'A:
Ya Ubangiji, ka cika ni da hikimarka kuma ka ba ni karfin hali in zabi rayuwar yabo, godiya, da zama albarka ga wasu, cikin sunan Yesu. Amin.
ABINCIN YINI - 2026