F.a.g Of Jibwis Lugbe Division Abuja

F.a.g Of Jibwis Lugbe Division Abuja The society for Removal of Heresy & establishing sunnah. First Aid Group of Jibwis.The society for Removal of Heresy & establishing sunnah

03/04/2025

Akwai wasu makiya Allah da suke ɗauko tsoffin karatu na bidiyo da shugaban mu Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau yayi a baya, suna editing su yanko inda suke so, su sanya wai da sunan ya bada Raddi akan cin mutunci da wani marar tsoron Allah mai suna Ɗan Bello yayi a kansa. Sheikh Bala Lau baiyi magana akan sa ba, kuma bazai yi ba, duk wani bidiyo da kuka gani kuyi watsi da shi, daga makiya Allah yake, kuma shi zai mana maganin su insha Allah.

Jibwis Nigeria

Allah yakara lafiya da Nisan kwana
20/02/2022

Allah yakara lafiya da Nisan kwana

16/02/2022

WhatsApp Group Invite

ANYI JANA'IZAR BABAN MU, BABBAN MAI LADABTARWAR MAJALISAR AGAJI TA KASA   Malam AbdulQadir Adamu JegaA Birnin Sokoto dak...
04/05/2020

ANYI JANA'IZAR BABAN MU, BABBAN MAI LADABTARWAR MAJALISAR AGAJI TA KASA

Malam AbdulQadir Adamu Jega

A Birnin Sokoto dake Jihar Sokoto, Ina yiwa Dukkan 'yan Agajin Nigeria da Africa baki daya Ta'aziyyar wannan Babban Rashi da mukayi, Da fatan Allah Ya Gafarta masa, Allah ya bamu hakurin wannan rashi.

Shehu A. Abdurrahman Gashua
Assistant National Organising Secretary

INNAA LILLAAHI WA INNAA ILAIHI RAJI'UN !!!    DARAKTAN AGAJI NA KASA JIBWIS          Engr. Mustapha Imam Sitti          ...
04/05/2020

INNAA LILLAAHI WA INNAA ILAIHI RAJI'UN !!!

DARAKTAN AGAJI NA KASA JIBWIS

Engr. Mustapha Imam Sitti

Na sanar da Ku rasuwar
MAL. ABDULKADIR ADAMU JEGA National Discipline Officer

wadda ya rasu ranar Lahdi 3/5/2020. Za a yi Jana'izarsa yau Litinin 4/5/2020 da 9:00 A.m. (na Safe) a Birnin SOKOTO in shaa Allah. Allah yaji kansa ya kuma gafarta masa.

(Dep. Nat. Pub. Sec.)
Muhammad Nura Abdullahi

JIBWIS TA DAKATAR DA TURA MALUMA WAJEN TAFSIRI A FADIN NAIJERIYA DA KASASHEN AFURKAShugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala...
17/04/2020

JIBWIS TA DAKATAR DA TURA MALUMA WAJEN TAFSIRI A FADIN NAIJERIYA DA KASASHEN AFURKA

Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bayyana matsayar da Ƙungiyar Izala ta dauka na dakatar da tura malamai Tafsirin Ramadaan na shekarar bana 1441/2020 daga jiha zuwa jiha da kuma zuwa kasashen waje sak**akon annobar cutar Coronavirus wacce likitoci s**a tabbatar tana yaduwa a duk lokacin da mutum ya kusanci mai dauke da cutar.

Kungiyar ta umurci mabiyan ta da su dukufa da addu'o'i musamman a cikin watan Ramadaan mai cike da falala wanda Allah yake karban addu'an bayin sa a ciki. Jihohi da suke da dokar takaita zirga zirga(lock down) malaman da ke jihohin zasu gudanar da Tafsiri a kebantaccen wuri tare da masu dauka (recording) ba tare da mutane sun halarta ba.

Mutane zasu iya kallo a gidajensu ta hanyar Manara Tv, shafukan kungiya na social media da sauran kafafen yada labaru.

Wa'azin kasa a garin Azare jihar Bauchi..........Shugaban ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah wa iƙamatis Sunnah ta ƙasar ...
17/11/2019

Wa'azin kasa a garin Azare jihar Bauchi..........

Shugaban ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah wa iƙamatis Sunnah ta ƙasar Naijeriya Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, a madadin ƙungiyar wacce Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo ke shugabantar majalisar Malamai, Injiniya Mustapha Imam Sitti ke jagorantar majalisar Agaji, na farin cikin gayyatar ƴan uwa musulmi zuwa wajen wa'azin ƙasa da ƙungiyar zata gabatar a garin Azare (Katagum) a jihar Bauchi a tarayyar Naijeriya a ranakun Asabar da lahadi 23/24-November-2019 Insha Allah.

kaɗan daga cikin Malaman da ake saka ran halartan su tare da gabatar da wa'azi, sun haɗa da;

-Ash-Sheikh (Dr.) Abdullahi Bala Lau
-Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
-Sheikh Usman Isa Taliyawa Gombe
-Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina
-Sheikh Abbas Muhammad Jega
-Sheikh Barr. Ibrahim Sabi'u Jibia.
-Sheikh Habibu Yahaya Ƙaura
-Sheikh (Dr.) Muhammad Kabir Haruna Gombe
-Sheikh Dr. Abdullahi Saleh Pakistan
-Sheikh Abubakar Giro Argungu
-Sheikh Gambo Kyari Maiduguri
-Sheikh Abdulbasir Isah Unguwan Mai kawo
-Sheikh Khalid Usman Khalid Jos.
-Sheikh Engr Aliyu Burga Azare
-Sheikh Mukhtar Zinder
-Sheikh Dr. Isma'il Kumo
-Sheikh Abdullahi Telex Zariya
-Sheikh Abdussalam Abubakar Baban Gwale
-Sheikh Jamilu Albani Samaru Zariya
-Sheikh Ibrahim Idris Zakariyya jos
-Sheikh Musa Yusuf Asadus Sunnah
-Sheikh Aliyu Adarawa
-Sheikh Dr. Ibrahim Abdullahi R/Lemo.
-Sheikh Dr. Abdulkadir Saleh Kazaure
-Sheikh Dr. Rabi'u Umar R/Lemo
-Sheikh Dr. Abubakar Riba
-Sheikh Imam Ibrahim lawal Osama Abuja
-Sheikh Muhammad Kabir Ahmad Azare
-Sheikh Aliyu Sa'id Gamawa

Da Alarammomi k**ar su;

-Alaramma Abubakar Adam Katsina
-Alaramma Ahmad Suleiman Kano
-Alaramma Nasiru Salihu Gwandu
-Alaramma Abdulkarim Akwanga
-Alaramma Bashir Abubakar Gombe
-Alaramma Ilyas Birnin Gwari
-Alaramma Usman birnin kebbi
-Alaramma Ibrahim Yahuza Bauchi
-Alaramma Auwal Unguwar Maikawo
-Alaramma Saifullahi Kira
-Alaramma Yusuf Ahmad Dabai
Alaramma Suleiman Abdullahi Azare
Alaramma Abdul'azeez Abubakar Azare

-Manyan Masu masaukin Baki, Maigirma gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Bala Muhammad Kauran Bauchi.

-Mai martaba Sarkin Katagum, Alhaji Umar Kabir Umar II.

-Shugaban JIBWIS na jihar Bauchi, Alh. Inuwa Dan'asabe.

Sanarwa daga ofishin Sakataren kungiya ta kasa, (Secretary General) Sheikh (Dr.) Muhammad Kabir Haruna Gombe.

Ta Ofishin Kula da harkokin yanar gizo ta JIBWIS, (JIBWIS Social Media.)

AIKIN AGAJI DA YADDA DAN AGAJI YA KAMATA YA KASANCEDaga Ustaz IBRAHIM BABA SULEIMAN Godiya ta tabbata ga Allah, muna god...
14/11/2019

AIKIN AGAJI DA YADDA DAN AGAJI YA KAMATA YA KASANCE

Daga Ustaz IBRAHIM BABA SULEIMAN

Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman tsarinsa daga sharrukan kawunanmu da miyagun ayyukanmu. Ina shaidawa babu wanda ya cancanci a bauta mawa sai Allah. Kuma ina shaidawa Annabi Muhammad (SAW) bawan Allah ne kuma Manzon Allah ne.

Abun da ake nufi da Agaji shi ne taimako, idan an ce Dan Agaji, to wani mutum ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin ya taimakawa dukkan wanda ke bukatar taimako.

Sannan dole ya zama mai iya Agajin ba wanda za a Agaza masa ba. Dan Agaji ya na taimakawa wanda hadari ya rutsa da shi wajen ba shi taimakon farko wanda a turance ake cewa (First Aid) wannan hadari na jirgi ne ko mota ko babur ko keke da sauransu, sai kuma abin da ya shafi gobara, annoba, ambaliyar ruwa da mak**antansu.

To a irin wannan lokaci Dan Agaji Zai bada taimakon farko kafin akai majinyaci asibiti ta hanyar tsaida jinin dake zuba daga rauni, a tsaftace wajen, sannan a daure da kyalle mai kyau don hana shigar wata cutar daban.

Baya ga haka kuma Yana daga cikin Ayyukanmu idan za a yi wa’azi ko wani taro na addini, dan agaji ne ke fara zuwa wajen don gudanar da shirye-shirye wajen saukaka cunkoso ga jama’ar da za su zo a yayin taron, Sannan a samar da tsaro tare da daidaita kayayyakin wa’azi, samar da haske, kayan sauti da sauransu.

Ire-iren wadannan bukatu kungiyar Izala ta ga dacewar kirkiro rundunar Agaji da za ta yi aiki tukuru tun fiye da shekaru 30 da s**a gabata. Tun lokacin wannan runduna ta fara gudanar da ayyukanta, sannan kuma ta ke kokarin inganta tsare-tsarenta a kullum don dacewa da kunkiyoyin duniya daban-daban k**ar yadda ake gani a yau.

Baya ga shirya taruka da kuma wa’azi akwai kuma wani aikin da rundunar take gudanarwa don tallafawa al’umma?
Eh! Akwai mana, Sosai ma kuwa, ita wannan runduna ayyukanta a tsare suke k**ar yadda na bayyana cewa idan hatsari ya rutsa da mutum ko wane iri ne mu kan jajirce mu taimaka, sannan a lokacin aikin Hajji zaka ga 'yan agaji a sansanonin alhazai su na taimakawa a yayin tafiya kasa mai tsarki da kuma dawowa.
Don haka zaka ga al’umma ne daban-daban suke taruwa a filayen tashi da saukar jiragen sama, wasu daga kauyuka s**a fito ba su san ko ina ba, don haka ‘yan Agaji za su taimaka musu wajen nuna musu yadda za su yi har a cimma nasara. Sannan shi ma wayayye akwai fannonin da za a taimaka masa a sansanin kafin ya tashi zuwa kasa Mai Tsarki.

Sannan kuma muna Tafiyane karkashin doka, wadda bata sabawa shari'a ba, yana daga cikin Dokar agaji, wajibi ne idan ana gudanar da wani taro wanda yake halastacce na addini Wadda Uwar Kungiya Ta shirya dan Agaji ya je ya taimaka ya bada gudumawarsa . Kuma dukkan wani taro da addini bai yarda da shi ba ko da an danganta shi da addini to a wajen dan Agajin Izala haramun ne ya halarci taron.

Majalisar agaji takan Gayyato Hukumar 'Yan Sanda (Police), Hukumar Kiyaye Hadura (Road Safety), Hukumar Bada Agajin Gaggawa (NEMA), Hukumar Kashe Gobara (Fire Service), Hukumar kiyaye Sha da fataucin Miyagun Kwayoyi (N.D.L.E), Jami'an Kula da Lafiya (Health), Malaman Addini Masu Wa'azi, inda kowa Zai zo ya Karantar da yan Agajin Irin Gudunmawar da Dan Agaji Zai bada Yayin da ake Neman Taimakon Gaggawa a dukkan wadannan Fannoni da muka Zayyana Muku a sama, Domin Aikin Agaji abu ne da yake son a yawaita Muraja'ar sa lokaci bayan lokaci.

HALAYYAN DAN AGAJI
Akwai wasu halayya da ake bukatar dan Agaji ya dabi’antu da su. Na farko ya zama mutum ne mai tsoron Allah da akida, idan ka na da kyakkawar akida zaka iya yin mu’amala da kowane irin mutum, sannan dan Agaji ya zama mai hakuri da juriya ya zama maras tsoro.

Idan dan Agaji ya siffantu da wadannan siffofi, to duk yadda mutum yake za ka iya tunkararsa da irin halinsa, wani ya na da kaushi, wani ya na da sauki, to duka zaka yi ta kokari har akai ga samun nasara ba tare da Hankali yatashiba ba.

Dolene Danagaji ya kasance mai Hakuri a duk in da ya tsinci kanshi, Domin zaka fuskanci matsaloli da daman gaske kafin wanda kake wa hidima su fahimce ka, wani zai zage ka, wani ya renaka ka , Amma idan Kayi Hakuri sai kaga Kaine da riba
'dan agaji bashi da albashi kuma baya daukan makami da ya shafi bindiga ko wani makamin da hukuma ta hana. Haka zalka, dan agajin Naijeriya aikin sa ya shafi kasashen yammacin Afirka har ma zuwa Saudiyya da sauran kasashe, Aikin agaji aiki ne na sa kai, kuma dan agaji yakan taimaki duk mai bukatan taimako, domin mu a izala manufar mu shine, dukkan abin da dan agaji zai agaza ne ga dukkan musulmai wadanda s**a yi kalmar shahada, ma'ana aikin ya shafi kowane musulmi, har ma da wadanda ba musulmi ba in ta k**a.

TSARO A FILIN WA'AZI
Ana so Dan agaji ya Kula da caje jikin duk mai zuwa masallaci tun daga nesa.
Kula da duk motocin da s**a zo musamman in aka ga tsohuwar mota mai bakin gilashi da sabbin tayoyi.
Lura da mutanen da s**a sanya kayan da basu dace da yanayin da muke ciki ba k**ar;

i) Cunkusa kaya a jiki
ii) Yawan sanya hannu cikin Aljihu.
iii) Kokarin kauce ma masu bincike.
iv) Kokarin kutsawa kai cikin jama'a da kuma yawan tsarguwa (rashin natsuwa)
v) Lura da wayar wuta a wuyan mutum ko kasan rigar shi.
vi) Kula da alamun warin wani sinadari (Chemical) a jikin mutum.

Dole a samu mata da zasu duba mata 'yan uwan su, suma daga nesa da jama'a (a sa gate tun daga nesa).
Kowace mace sai ta daga abayar ta tun daga nesa.
Kula da mutane masu zuwa da leda ko kunshin kaya.
Kula da harabar masallaci da duk wani kunshin kaya da za a iya gani a masallaci.
A fadakar da yara game da tsince-tsincen kunshin kaya da za su iya gani a harabar masallaci.

*PROTOCOL
Ana bukatar dan agaji ya zama na farko a duk wani taro na kungiya, sannan ya zama mai karban baki da basu wurin zama, basu ruwan da zasu sha da sauran dawainiya, musamman in an ajiyeka a wannan bangaren.

*DABI'UN DAN AGAJI
Ana bukatar dan agaji ya zama mai k**ala, mai nutsuwa, mai dattaku, domin in samu akasin wannan, ba kai dan agaji za'a duba ba, kungiyar Izala za'a duba, domin kai Babban wakili ne na kungiyar a duk inda ka samu kanka

*Idan mutum ya na son zama xan Agaji, wadanne qa’idoji ya k**ata ya bi don zama xan agajin Izala?

To Alhamdulillahi, wannan qungiya mai albarka ta na da tsari da kuma qa’idoji a kowane fanni na ta. Da farko idan mutum ya na son ya zama xan Agaji a wannan qungiya, to dole ya zama ya na da kyakkyawar aqida wacce ba a gurvata ta da komai ba. Sannan na biyu dole sai ka samu tazkiya daga mai unguwarku wacce za ta tabbatar mana cewa kai mutumin kirki ne ka na da riqon amana da sauransu. Sannan na uku dole ya zama ka na da sana’a ba zaune kake ba, ma’aikacin gwamnati ne ko xan kasuwa ko manomi ko mai sana’ar hannu. Idan kuma yaro ne qarami to ya zama ya na makaranta. Sannan na huxu dole ya zama ka na aji ko makaranta da kake karatu, saboda ba ma xaukar wanda bai san addini ba. Sannan na biyar ya zama wanda zai iya karvar horaswa ta yadda zai san qa’idojin aikin yadda ya k**ata. Sannan na shida za a yi ma sa jarabawa kan abin da aka koya ma sa idan ya ci shike nan ya zama xan Agaji. Sai na bakwai, xan Agaji shi da kan sa zai xinka kayan Agaji da duk wasu kayayyaki na aikin. Sannan na qarshe zai amince cewa idan Allah Ya masa rasuwa kayansa na Agaji ba na magada ba ne, za a dawo da su a baiwa wani ya ci gaba da amfani da su, shi kuma Allah Ya ba shi ladar a makwancinsa. Haka nan Allah Ya sawwaqa idan ya aikata wani laifi da za a kore shi nan ma zai dawo da kayan Agajinsa a baiwa wani yaci gaba da amfani da su. To waxannan su ne qa’idojin zama xan Agaji a taqaice.
Sannan har ila yau akwai dattijo xan shekaru 60 ko 70, sannan kuma sai aga yaro xan shekaru shida ko bakwai, shin ya tsarin xaukar aikin yake a matakin shekarun yaro, ko kuma na yin ritaya ga wanda ya tsufa?

To aikin Agaji dai ana son mutum Baligi mai hankali, wanda za a iya sanya shi ko wane irin aiki, sannan zai iya wakiltar qungiyar a kowane lokaci. Amma a qasa k**ar yadda muka faxi cewa akwai yara qanana, e, haka ne, mu na da wani mataki na xaukar yara qanana saboda koyar da tarbiyya, mu yi mu su tirenin mu ba su tarbiyya su taso a haka. mu na xaukarsu saboda dalilai k**ar haka; Na farko za su samu tarbiyyar da za su amfani iyayensu, saboda ba su da kasala, don haka za su je aika, xiban ruwa, kai niqa da sauransu. Domin idan yaro ya saba da aikin Agaji, to babban abin ba ya so shi ne ace za a qwace inifom xinsa, don haka duk wanda aka kawo rahoton ya qi yin aika a gidansu idan aka yi ma sa barazar qwace inifom xin sa sai ya yi ta kuka sannan ya yi alqawarin zai gyara halayensa. Na biyu mu kan yi amfani da yaran don burge jama’a a wajen taruka, wajen sanya su yin dirama ko fareti mai ban sha’awa. Sannan na uku za su ta so da tsoron Allah da riqon amana.

Sai kuma maganar ritaya, gaskiya mu ba mu da wani matakin yin ritaya a wannan aikin saboda shekarun mutum, sai dai ba ma xaukar mutum a karon farko idan shekarunsa s**a kai 50 ko 60, saboda a lokacin ya fara rauni. Amma idan ya fara aikin tun ya na matashi, to ba za mu yi ma sa ritaya saboda tsufansa ba, sai dai za a sanya shi aiki irin wanda ya dace da shi, tunda aiki ne na addini ba ka hana mutum samun alherin dake cikinsa, sai ya yi ta yi har Allah Ya xauke shi.

*Yadda tsarin qarin girma na agaji yake a wannan aiki
To wannan runduna a qarqashin qungiyar Izala mun kasa muqamai ne zuwa kashi shida. Akwai abin da muke kira ‘unit’ ko wane unit akwai adadin ‘yan Agajin da suke wurin, idan s**a wuce wannan adadin sai su zama ‘Detachment’ daga nan kuma sai ‘Division’ sai qaramar hukuma, sai jiha, sannan matakin qasa gaba xaya. Don haka daga kan ‘Unit’ din nan akwai shugaba akwai mataimakin shugaba, akwai sakatare, akwai sakataren tsare-tsare da sauransu. Haka nan dukkan waxanna matakai akwai shugabanninsu har zuwa kan Daraktan jiha zuwa Babban Darakta na qasa. Sannan mutum ya na samun qarin girma ne bisa cancanta, ilmi da kuma qwazonsa wajen aiki.

A sau da dama Malamanku na Izala s**an yi s**a ga ‘yan siyasa, musamman a lokacin zave, inda waxansu ‘yan siyasar ke yin hayar matasa da za su riqa kawo cikas ko su sace akwatin zave da sauransu, shin ku na da wani tunani wajen sanya jami’anku na Agaji su riqa bayar da tsaro a lakacin zave ko kuwa?
A’a la! Wannan qungiya ce ta addini ba ta siyasa ba. Don haka ba mu da wani tunani na aika ‘yan agajinmu wajen tsaron akwati a lokacin zave. Amma k**ar yadda muka ce, wannan qungiya ta na faxa da irin wannan xabi’a na rashin adalci, sannan gazawar gwamnati wajen samar da tsaro shi yake kawo haka, domin duk mutum quri’a guda yake da ita, amma idan gwamnati ta tsare wannan amana dake kanta, babu yadda za a yi irin haka ya ci gaba da faruwa a qasa irin Nijeriya.
Sai dai k**ar yadda wasu ‘yan siyasar s**a xauki matakin cewa, a kasa a tsare a raka, to wannan ba aikin xan Agaji ba ne, na dukkan al’umma ne, kar ka manta xan Agaji ya na da yancin da zai je ya jefa quri’a kuma ya sa ido wajen ganin an yi ma sa adalci ga wanda ya zava, amma ba da sunan Agaji ba, zai je ne k**ar kowa cikin kayan gida ya jefa quri’a rsa ga wanda yake so.

*NASARAR AIKIN AGAJI:
Zuwa yanzu an samu nasarar cikakken biyayya tare da doka da oda a cikin aikin agaji, kuma duka wannan ya biyo bayan tsarkake niyya ce wanda Allah ya gani yake kawo mana gudunmawa a cikin wannan aiki.

*MATSALAR AIKIN AGAJI:
Matsalolin da ake samu a aikin agaji sune riga malam masallaci,, tare da rashin tsayawa a koyi aikin agajin tare da bin dokokin sa k**ar yadda yake a tsare.
Sannan a wani sashi daga cikin Constitution inda aka rubuta a maganar karshe a (iv) CLOSING REMARKS watau jawabin RUFEWA k**ar haka:-
{Muna kara tabbatar wa jama'ar Musulmin Duniya cewa, wannan kungiya tamu ta Izala kungiya ce da aka kafa ta domin ta karantar da jama'ar Musulmi ta hanyan yi musu wa'azi da kuma kafa makarantu, ita ba kungiya ba ce ta siyasa, ba kuma kungiyar asiri ba ce, haka kuma ba ta darika ba ce ko wace iri, ita dai kungiya ce ta addinin Musulunci tsantsa k**ar yadda Annabinmu Muhammad (S.A.W.) ya taho da shi. Haka kuma ba ruwanta da tilasta ma wani ko wassu zamowa dan ko yan wannan kungiya k**ar dai yadda ya riga ya gabata a can sama, wannan kungiya dai ba hukuma ba ce, haka kuma ba ruwanta da shishigi a harkar hukuncin kasan nan ko wata kasa, wanda ta kasance akwai yan wannan kungiya a cikinta, (manufa dai ita wannan kungiya ba ta da ikon hana hukuma yin hukunci a kan dan wannan kungiya a lokacin da duk aka same shi da wani laifi a cikin kasan nan ko wata kasan). Kuma duk mutumin da ya yi Imani da Alkur'ani da hadithan Annabi Muhammad (SA.W.) da kuma Ijma'in Malamai na kwarai, to ko a dokan daji yake shi kadai babu shakka dan wannan kungiya ne. Haka kuma matukar yana sauraron wa'azinta babu shakka yin haka ma taimakawa ne. Ita dai wannan kungiya ba da wani kati ko wata shaida na nuna cewa lalle sai ka yi rajista matukar dai ka yi Imani da abin da aka fadi a sama to babu shakka Kai dan wannan kungiya ne. Kuma sannan kowa na da hakkin ba wa kowa shawara, ko nasiha ko mai girman wanda za a yi wa nasihar ko ba da shawarar, ko mai kankantar shi mai nasihar ko shawaran matukar yin shawarar ko nasihar an yi yadda Musulunci ya shirya abubuwa}.
Zamu karkare da maganar tsoron Allah ga 'dan agaji :
ANNABI S.A.W YA CE "ALLAH TA'ALA YA CE:
[Na rantse da IZZATA bazan hadawa Bawana tsoro biyu ba hak**a bazan hada masa aminci biyu ba:
Idan yaji tsorona aduniya- to zan amintar dashi alahira
Idan kuma ya amintu a duniya baiji tsorona ba- to zan tsoratar dashi alahira]
[SILSILATUL AHADEETSUS SAHEEHA=2666]

To Dan'uwana- kaji tsoron ALLAH anan duniya don ya amintar dakai daga dukkannin tsoro da barazanar wuta alahira, shiyasa ALLAH yace= (wanda "yaji tsorona" yabi shiriyata babu tsoro a kansuz a lahira kuma babu bakin ciki) [S/BAQARA=38]

YA Allah kacusa mana tsoronka anan duniya mubi dokokinka, kuma ka-amintar damu daga tsoro da firgici da barazanar shiga wuta agobe kiyama.
AMEEN

Dan uwanku a musulunci.
Ibrahim Baba Suleiman
Mai baiwa shugaban agaji shawara akan harkokin yada labarai

Hotuna: Ziyarar girmamawa da Vise Chensalor na Islamic University of Uganda Dr. Ahmad Kawesa sengendo ya kawo ofishin sh...
03/09/2019

Hotuna: Ziyarar girmamawa da Vise Chensalor na Islamic University of Uganda Dr. Ahmad Kawesa sengendo ya kawo ofishin shugaban JIBWIS na kasa, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau a sakateriyar kungiyar take birnin Tarayya Abuja.

Address

Amac C, Lugbe Division Office Airport Road
Abuja

Telephone

08163927986

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when F.a.g Of Jibwis Lugbe Division Abuja posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to F.a.g Of Jibwis Lugbe Division Abuja:

Share