30/12/2025
BAYANI GAMEDA DARUSSAN DA A KE KOYARWA A AL-TASFIYAH ONLINE ACADEMY
1- QUR'AN STUDIES FOR BEGINNERS (2 Months Duration): a wannan bangaren za a karantar da Al-Qur'ani Tartilan da Tajwidi da ilmomin da ke da alaka da Al-Qur'ani.
Registration fees: 1,500
Monthly fees (Tuition): 1000
Certificate fees: 200
Total: 3,700
2- ISLAMIC STUDIES FOR BEGINNERS (3 Months Duration): a wannan course za'a karantar da Tauhidi, Hadithi, Sirah da Fiqhu a matakin farawa. Maksudin wannan course shi ne karantar da ilimin addini da yadda za a bautawa Allah.
Registration fees: 1,500
Monthly fees (Tuition): 1000
Certificate fees: 200
Total: 4,700
3- ARABIYYA: Course not yet available.
WASU TAMBAYOYI DA AMSOSHIN SU:
1- Tambaya: Shin a ina ne a ke gabatar da karatun?
Amsa: a WhatsApp da Telegram
2- Tambaya: Wata nawa ne kafin a kammala karatun?
Amsa: ya danganta da course da ka ke, idan Al-Qur'ani ne da tajwidi wata biyu, idan kuma Islamic Studies ne wata uku.
3- Tambaya: Shin idan mutum ya biya kudin rijista zai sake biyan wani kudi?
Amsa: Eh, da farko za ka biya naira 1,500 kafin ka shiga aji, daga nan duk bayan wata daya za ka biya dubu daya, har ka kammala karatun, kaman dai yadda a ke da kudin rijista da kudin term a makarantan boko, sai lokacin da a ka yi jarabawar karshe za ka bayar da naira 200 kacal na certificate. Idan ka ga dama kuma, za ka iya ka lissafa wata nawa ne course dinka, sai ka yi total na kudin ka biya gaba daya kafin a fara karatu daga nan ba sai ka kara biyan ko sisi ba har a kammala.
4- Tambaya: Shin malamai nawa ne a kowane course?
Amsa: ya danganta da yawan subjects da ke karkashin wannan course din, kowane subject ya na da malamin da ya ke karantar da shi.
5- Tambaya: Shin idan ina da uzuri bansamu daman shiga aji a kan lokaci ba yaya zan yi?
Amsa: za ka samu Audios da videos da a ka ajiye a kan group sai ka bibiya, shikenan kai ma ka samu karatun ranan.
6- Tambaya: shin a na yin live ne a karatun?
Amsa: Eh, akwai ranaku da za a ware na musamman a sati ko a wata a kowane subject da za a rika yin live session tsakanin Malamin subject da dalubansa, amma ba kullum ba ne, shi wannan a na yi ne domin kara inganta alakan Malamin da daluban da kuma samun daman tambayoyi na kai tsaye.
Domin yin rijista danna wannan link ɗin
https://forms.gle/MpN9F1A3q2vhsEGf6
✍️ C.E.O Al-Tasfiyah Online Academy
Anas Salihu Muhammad