20/06/2022
Mu'awiyyatu bn al-hakam Assulamiy- RadiyalLahu anhu ya ce: Ban taba ganin wani malami kafinsa haka nan bayansa mafi iya koyarwar kamar Manzon Allah -SallAllahu alaiHi wa sallam ba. Bai min tsawa ba, Bai duka ni ba, Bai zageni ba.
Lokacin da nai magana ana sallah, cemin kawai ya yi bayan idar da sallah: "Lalle cewa ita wannan sallar ba wani abu na zantukan mutane da ya inganta ayi cikinta, cewa ita Tasbihi ce da Takbeeri da Karatun Al'Qur'ani.
Sai na ce ya Manzon Allah: Daga cikinmu akwai Wasu mazaje masu zuwa gun bokaye?
Sai ya ce: Kar ka je musu.
Kissar tana da tsayi.
Na ce: Ya kake tunani yau idan wani ya he masallaci ya Yi fitsari, ko ya K**a surutu ana sallah, ko ya ce ww malam yana zuwa gun boka?!