Jibwis Kuje Area Council Media

Jibwis Kuje Area Council Media Official Jibwis Kuje Area Council Media page for the propagation of Islam & it's activities!
(2)

19/03/2026

Za'a tsaida Sallar Idil-el-Fitr karfe 9:15am a Masallacin Idimmu dake Kuje Insha'Allah📌

14/03/2026
Yau Kungiyar Izala Ta Cika Shekaru 48 Da KafuwaA ranar 12 ga watan Maris 1978, aka kafa Kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'...
12/03/2026

Yau Kungiyar Izala Ta Cika Shekaru 48 Da Kafuwa

A ranar 12 ga watan Maris 1978, aka kafa Kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa'Ik**atus Sunnah (JIBWIS).

JIBWIS Ƙungiyar Addinin Musulunci ce, mabiya Sunnar Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi. Sannan kuma an kafa wannan ƙungiyar ne a babban Birnin Jihar Plato da ke Jos, wanda babban malamin Musulunci kuma Babban Hafsan Sojan Najeriya ya kafa, wato Sheikh Ismaila Idris Bin Zakariyya Jos wanda kuma har yanzu Cibiyar Gudanarwa na kungiyar yana garin Jos a karkashin jagorancin Khalifa na farko na wannan ƙungiya wato Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir.

Daga cikin muhimman manufofin wannan ƙungiya sun hada da:

1. KaÉ—aita Allah da bauta ba tare da haÉ—a Shi da wani ba (shirka). Sannan a tabbatar da biyayya ga Annabi Muhammad (SAW) ba tare da jayayya ko kawo maganganun wasu mutane na daban ba.

2. Tabbatar da bin ɗabi'un (sunna) Manzon Allah (SAW) ba tare da ƙirƙire-ƙirƙire ba.

3. Watsi da dukkan al'adun da s**a saɓa ma addinin Islama.

4. Soyayyar Annabi (SAW) da iyalan shi da sahaban shi /abokan shi da kuma surukan shi ba tare da s**ar ko É—aya daga cikinsu ba.

5. Tabbatar da neman ilimin addini da na boko a ko'ina a faÉ—in duniya tare da bin dokokin addini.

6. Tabbatar da mutuncin waliyyan Allah na gaskiya da salihan bayi da duk sauran mutanen kirki.

Yau Shekaru 48 daidai da kafa kungiyar Izala wadda Sheikh Ismail Idris Bn Zakariya ya kafa ta a garin Jos, kuma ya jagorance ta har zuwa karshen rayuwarsa.

Malam ya sha gwagwarmaya daga makiya sunnah a wancan lokacin, har yunkuri kashe shi an yi, ya je gidan yari a sanadiyyar wa’azi.

An taba k**a Sheik a garin Kano daga can aka wuce da shi Cross River (Calabar) sai da ya yi kwana 40 ba a san inda yake ba.

Saboda wa’azi Sheik ya bar aikin soja. An sha fama sosai wanda wani garin ma idan s**a je wa’azi ana hana su, misali wata rana an je wa’azin kasa Maiduguri, ana dab da shiga garin Maiduguri domin wa’azi sai aka ce ba za a shiga ba, Sarki ya hana duk da cewa a wancan lokacin sai an nemi izini a wajen hukuma kafin zuwan su, amma duk da hakan aka hana su karshe dai Sheikh ya bawa jama’a hakuri aka koma gida.

Sheikh ya yi rayuwa abin koyi da burgewa a matsayin sa na Malamin addinin Musulunci. Duk girman ka Mal zai fada maka gaskiya ba tare da tsoro ba.

Allah muke roko da ya lullube shi da rahmar sa, Ya sa ya huta idan ta mu ta zo Ya sa mu cika da Imani.

06/03/2026
KAI TSAYE DAGA GARIN JOS: KWAMITIN TAFSIRIN IZALA NA YOBE YA ZIYARCI SHEIKH JINGIRA wani muhimmin lamari mai cike da zum...
03/03/2026

KAI TSAYE DAGA GARIN JOS: KWAMITIN TAFSIRIN IZALA NA YOBE YA ZIYARCI SHEIKH JINGIR

A wani muhimmin lamari mai cike da zumunci da hadin kai, Kwamitin Tafsirin Kungiyar Izala na Jihar Yobe, Damaturu, sun kai ziyara ta musamman ga Fadilatush Shaykh Muhammad Sani Yahya Jingir a garin Jos.

Ziyarar ta kasance wata alama ta girmamawa, tuntuba, da karfafa dankon zumunci tsakanin malamai da kwamitocin tafsiri na jihohi daban-daban karkashin inuwar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS).

Sheikh Muhammadu Sani Yahya Jingir ya karbi bakuncin kwamitin cikin karamci da fara’a, inda ya gabatar da jawabai masu cike da hikima, nasiha, da jan hankali kan muhimmancin tafsirin Alkur’ani, hadin kai, da tsayawa kan koyarwar Sunnah. Ya jaddada bukatar tsarkake niyya, dagewa wajen yada ilimi, da kula da tarbiyyar al’umma musamman a lokutan da ake bukatar shiriya da jagoranci.

Wannan ziyara ta kara tabbatar da irin kyakkyawar wakilci da hadin kai da ke tsakanin shugabannin da malaman Izala a matakin kasa da jihohi, tare da nuna goyon baya ga jagoranci da shawarwarin malamai.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya saka da alkhairi ga dukkan mahalarta wannan ziyara, Ya kara wa malamai lafiya da basira, tare da dawwamar da hadin kai a cikin wannan gagarumin aiki na yada tafsirin Alkur’ani da koyarwar Sunnah. Ameen.

24/02/2026

Mr Emmanuel Dan Allah ya shiga Musulunci, Mai girma CP ina gaiyatarka zuwa Addinin Musulunci -Dr Alkali A.S Zaria 🤭

Address

Junior Staff Quarters Kuje Area Council
Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis Kuje Area Council Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Jibwis Kuje Area Council Media:

Share