17/05/2026
Sanarwa:
AN GA JINJIRIN WATAN ZHUL HIJJAH 1447
Daga: Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H).
بِسْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ
اللهم صل على محمد وعلى آل محمد🌹
Ya zuwa yanzu mun sami labarin tabbacin ganin jinjirin watan Zhul Hijjah a cikin garin Mafara a wata unguwa da ake kira Kartawa da wasu ƙauyuka da ke kewaye da Mafara kamar Birnin Wake, Basara Ƙarama da Basara Babba. Har wala yau an gani a garin Ɗandume. Duk a waɗannan wurare ƴan'uwa ne da jama'a masu yawa s**a ga jinjirin watan.
Don haka gobe Litinin za ta zama 1 ga watan Dhul Hijjah 1447, in sha Allah.
Kada a manta da ayyukan kwanuka goma na wannan wata wadda Allah Ta'ala ya kira su layalul ashar (ليال العشر) a Suratul Fajr. Da kuma ladubban layya don tunawa da sadaukarwar Annabi Ibrahim (AS).
Allah ya ba mu sa'a.
Wassalam
29/Dhul Qa'adah/1447
17/May/2026