09/02/2014
RAHOTO DAGA JARIDAR RARIYA: Cikakken Rahoto Kan Yadda Aka Kashe Sheikh Auwal Albani Zariya
Daga Ibrahim Ammani, Kaduna
“Mu duba dai ga sarakunanmu, wadanda sunka rike kasarmu, yau ina su Shehu Mujaddadinmu, mu sani ba zamu dawwama ba.”
Wannan wani baiti ne daga cikin baitoci na wakar Infiraji, wanda dattijon nan marigayi Malam Aliyu Namangi Zariya ya rera a zamanin rayuwar shi.
Kuma wannan waka ta Infiraji daya ce daga cikin wakokin da sanannen malamin nan, mazaunin unguwar Mucciya dake sabon garin Zariya, ke yawan bada misalai da ita, a mafi yawancin wa’azuzzuka da yake gabatarwa a majalisi daban daban, wato Abu Abdurrahman, Muhammad Auwal Adam Albani Zariya.
A karshen makon daya gabata ne wasu ‘yan Bindiga, da ba’a san ko su wane ne ba, s**a yi kwanton bauna s**a harbe shi tare da matarsa da daya daga cikin ‘ya’yansa, a lokacin da yake kokarin shiga gidansa, jim kadan bayan dawowarsa daga bada karatu, wanda ya saba yi a masallacin Juma’a na Salafiyya dake titin Maje Sabon Garin Zariya.
Ga dukkanin mutumin da ya san Auwal Albani, ya san shi a matsayin wani mutum mai jajircewa da kokarin fadin gaskiya komai dacinta, sannan a hannun guda, Albani mutum ne mai tsanani ga dukkanin wani wanda s**a saba da shi ta bangaren akida.
Auwal Adam, ya samo lakabin sunanshi na Albani ne, daga wajen fitaccen malamin nan, mazaunin Saudiyya, marigayi Alsheik Nasirudeenil Albani, wanda ya rasu wasu shekaru da s**a gabata.
Albani ya yi fice, wajen bada fatawowi sababbi wadanda ake ganin cewar sun saba da mazhabar da jama’a s**a gada iyaye da kakanni a tarayyar Nijeriya, wato mazhabar Malikiyya. Wasu daga cikin fatawowin da malamin ya bayar sun hada da halarcin gabatar da sallar Juma’a da sanyin safiya, sannan da wajabcin cin naman doki, da kuma mas’alar saki uku ga mace a lafazi guda, cewa yana matsayin saki guda ne, da saurana mas’aloli da ake wa kallon baki ne a addini.
Adam Albani ya sha amsa gayyata zuwa fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau, domin amsa tambayoyi daga bakunan malaman Zazzau, bisa kan wadannan fatawowi da yake bayarwa.
Lokacin da sunan kungiyar nan ya bayyana a Nijeriya, wato Boko Haram a shekarar 2009, karkashin jagorancin Muhammad Yusuf, Albani ya kasance a sahun gaba, wajen caccakar wannan akida, da kuma s**an lamirin shugabanta Muhammad Yusuf, wanda ya bayyana a matsayin wanda ya sani ciki da bai.
Albani ya amsa gayyata daga gwamnati akan wasu kalamai da ya furta wadanda ake ganin suna da nasaba, da taba sha’anin tsaro har sau biyu, kafin daga bisani kotu ta wanke shi, ya dawo ya ci gaba da ayyukan shi k**ar yadda ya saba.
A mafi yawancin lokuta Albani, na nesantar da kanshi daga dukkanin wata kungiya ta addini, inda yake bayyana kanshi a matsayin mai bin tafarkin magabata kawai, (SALAFIYYA) lamarin da ya bambanta shi da sauran takwarorinsa malamai masu da’awar Sunnah a tarayyar Nijeriya. Auwal Albani ya yi fice wajen s**an lamirin shugaban mabiya mazhabin Shi’ah a tarayyar Nijeriya,wato Alsheik Ibrahim Yakub El-Zakzaky, abinda masu nazari ke ganin cewar ba shi yiyuwa, tarihin daya daga cikinsu ya cika, ba tare da an ambato sunan dayan ba, wanda ba ya rasa nasaba, da kasanacewarsu manyan malamai na akidu biyu na musulunci, Sunnah da Shi’ah da ke zaune a gari guda.
Lokacin da wasu ‘yan bindiga s**a harbe, sanannen malamin nan mazaunin birnin Kano, Shiek Ja’afar Mahmud Adam, a shekarar 2007, Adam Albani ya kasance wanda ya fi kowa nuna takaici da damuwarsa akan wannan kisan gilla da aka yi, wanda hakan ta kai shi da shirya wata gagarumar Muhadara a shekarar 2009, mai taken “Waye ya kashe Malam Ja’afar?” Bayan kammala wannan muhadarar ne, malamin ya bayyana yadda ya yi ta samun sakwanni ta waya masu barazana ga rayuwar shi da ta iyalanshi a lokuta daban daban.
Sai dai tambayar da jama’a ke bukatar sanin amsarta ita ce, shin su waye ke da alhakin kaiwa malaman addinin musulunci hari akai akai haka? Bayan kisan da aka yi wa Malam Ja’afar a Kano, an yi nasarar hallaka Malam Muhammadu Dan Mai Shiyya, a garin Sakkwato, sannan sai ga na kwanan nan kisan Malam Albani a Zariya.
K**ar yadda bayanai s**a nuna Albani ya gabatar da wata Muhadara mai taken,”Ina Gaskiya Take Tsakanin Kur’ani Da Bible?” a ranar Juma’ar da ta gabata wato ranar jajibirin da za’a kashe shi wanda wani malami masanin Bilble mai suna Farfesa Dawud ya yi mishi ta’alikinta. Sannan a ranar Asabar a karatun da yake yi na Sahihul Bukhari a masallacin Markazul Salafiyya, malamin ya tsaya akan babin aikin Hajji, hadisi na karshe da ya karanta shine wanda ke bayanin wata mata ta tambayi Annabin Rahama (SAW) ko za ta iya yi wa mahaifinta aikin Hajji bayan rasuwarshi? Sannan malamin ya yi alkawarin gabatar da wata muhadara a ranar Lahadi da misalin karfe takwas na dare, mai taken “In Kun San Wata Ba ku San Wata Ba” muhadarar da bai sami gabatarwa ba kenan aka kashe shi a ranar Asabar da misalin karfe goman dare.
Akwai abin mamaki da ta’ajibi dangane da kisan da aka yi wa Sheik Albani, k**ar yadda wani makwabcin malamin yake bada shaida akan abinda ya ganewa idanuwanshi na abin tashin hankalin da ya faru. Ustaz Umar Ahmad yace sun hango wata mota baka kirar Jeep, tunda misalin 09:30 pm na dare, tana shawagi a kusa da gidan malamin, a daidai lokacin da Malam Albani yake dawowa daidai kwanar kofar gidanshi ne,wadannan makisa su biyar s**a afka wa motarshi da harbi gaba daya, kuma nan take s**a harbe matarshi mai suna Fatima, da danshi Abdullahi, a daidai wannan lokaci ne Malam Albani ya fara kira a gare su da cewar, kada su kashe kowa amma su kashe shi shi kadai, sun ci gaba da harbinsa ta ko’ina a jikinsa, kafin daga bisani s**a fito da shi daga cikin motar, s**a yi ta harbinsa, har sai da s**a tabbatar baya motsi, sannan s**a koma da gudu cikin motar tasu s**a gudu.
Bayan an kai shi asibiti ne ya cika sak**akon munanan raunukan da ya samu musanma a kan shi, wanda aka tabbatar da cewar an sami hujin harsasai sama da bakwai a kokon kan na shi.
Hankalin jama’a ya tashi matuka a lokacin da aka fito da gawar marigayin domin gudanar mata da sallar janaza, sak**akon yadda jini ya bata likkafinin malamin, a haka a gudanar masa da sallah shida iyalin tashi da kuma dan shi, kafin daga bisani aka binne su a makabarta.
Da yake bayyana yadda ya kalli wannan kisan gilla da aka yi, sanannen malamin addinin Islama mazaunin garin Jos,Alsheik Alhassan Sa’idu Jos, yace wannan kisan gilla da ake yi wa malaman addinin Islama, alama ce dake nuna cewar da akwai wata kullalliya daga karkashin kasa, da ake da ita na kawar da dukkanin wani malami mai fadin gaskiya a doron kasa, ya bada misali da kisan da aka yi wa Malam Ja’afar Adam, amma abin bakin ciki sak**akon rashin daukar matakin da ya dace, ya haifar da sake kai wani hari mak**ancinsa, indan kuma har ba’a gaggauta daukar matakiba, to abin zai ci gaba ne in ji malamin.
Shi ma da yake bayyana ra’ayinsa dangane da wannan jafa’i da ya faru, Alsheik Tukur Adam Almannar, yace wannan kisa da ake yi wa malaman musulunci a arewacin kasar, yana k**a da wani Bom da aka dasa a cikin al’umma da niyyar tarwatsa su, ta inda za’a kai ga wani matsayin da jama’a za su rasa jagora a addinan ce, wanda zai iya sa su a hanya madaidaiciya. Daganan sai ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar matakin binciko gami da kamo wadanda ke da hannu a cikin wannan aika aika domin hukunta su.
Rana daya bayan rasuwar Malam Albani tare da matarshi da dan shi guda, shi ma daya dan na shi mai suna Abdul Bari, ya rasu a washe gari sak**akon raunukan da ya samu a yayin harin, yayin da dayan dan na shi mai suna Abdul Hakk ke ci gaba da karbar magani a Asibiti.
Dubban jama’a ne daga sassa daban daban s**a halarci jana’izar tashi, wanda aka yi a gidansa dake Mucciya sabon garin Zariya, malamai da dama ne daga ciki da wajen kasar, s**a hallarci jana’izar, da dama daga cikinsu, sun kasa cewa komai sak**akon hawaye dake ta zuba a idanuwansu.
An haifi Malam Muhammad Auwal Albani a unguwar Mucciya dake yankin karamar hukumar Sabon Gari, a shekarar 1960, yayi karatunsa na Firamare a unguwar tasu, kafin daga bisani ya wuce kwalejin Barewa dake Zariya, sannan ya yi karatun digirin shi a jami’ar Ahmadu Bello Zariya, ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya da dama.